Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa

Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa

Jagorar kungiyar rajin ceto yan matan Chibok BBOG, Aisha Yesufu, ta caccaki gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, kan bayyana niyyarsa na rattafa hannu kan hukuncin kisan da akayiwa mawaki, Yahaya Sharif-Aminu.

Yahaya Sharif-Aminu dai ya yi maganar batanci ne ga Manzon Allah (SAW).

Aisha Yesufu wacce ta shahara wajen caccakan shugabanni ta yi jawabi a ranar Juma'a cewa shi ma Ganduje a yanke masa hukuncin kisa kan laifin karban rashawa.

Tace: "An kama Ganduje dumu-dumu kan Kamara yana karban cin hanci. A dokar Shari'a, duk kyautan da aka baiwa ma'aikacin gwamnati na gwamnati ne, ballantana karban cin hanci."

"Babu garkuwa a Shari'ar Musulunci. Ganduje ya kamata a yankewa hukuncin, ba shi ya rattafa hannu kan hukuncin kisa ba."

Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa
Ya kamata a yankewa Ganduje hukuncin kisa kan amsan rashawa
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukumar hana fasa kwabrin Najeriya watau Kwastam tayi gwanjon motoci 314 da kudinsu ya kai N152M

A ranar Alhamis, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis ya ce a shirye ya ke ya saka hannu domin a zartar da hukuncin kisar da kotu ta yanke wa mawaƙi Yahaya Sharif-Aminu da ya yi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).

Idan za a iya tunawa babban kotun Shari'a da ke Kano ta samu Aminu-Shariff da laifin batanci kuma ya yanke masa hukumcin kisa ta hanyar rataya.

A watan Maris ɗin shekarar 2020, mawaƙin mai shekaru 22 ya rera wata waƙa mai ɗauke da batanci ga Manzon Allah ya tura a dandalin sada zumunta ta WhatsApp, hakan ya sa mutane suka harzuƙa.

Da ya ke jawabi bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, Ganduje ya ce kotu ta bawa wanda aka yanke wa hukuncin wa'adin kwanaki 30 don ɗaukaka ƙara, idan bai ɗaukaka karar ba shi kuma ba zai bata lokaci wurin rattaba hannu a kan hukuncin ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng