Bidiyo: Yadda wani mutum ya riƙa kuka yana birgima cikin taɓo don budurwarsa ta ƙi yarda ta aure shi
An wallafa wani faifan bidiyon wani mutum ɗan Najeriya yana sharɓar kuka yana kuma birgima cikin taɓo bayan budurwarsa ta ƙi karɓar zoben neman amincewa ta aure shi.
A cewar rahotonni da aka wallafa, lamarin ya faru ne a cikin kasuwa da ke Owerri a jihar Imo.
A cikin bidiyon, ana iya ganin budurwar tana yi wa mutumin tsawa bayan ta ƙi amincewa da buƙatar suyi auren.
Shi kuma mutumin ya durƙusa har ƙasa ya fara roƙonta ta tausaya ta amince cewa za ta aure shi.
Lamarin daga bisani har ta kai ga ya fara birgima a ƙasa cikin taɓo duk da cewa yana sanye da fararen tufafi ne.
Mutanen da suka kasuwar sun yi ta ƙoƙarin shiga tsakani domin ganin budurwar ta taimaka ta amsa cewa za ta aure shi amma hakan ya ci tura.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC
Ga faifan bidiyon a kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng