Hukumar Kwastam tayi gwanjon motoci 314 da ta kwace

Hukumar Kwastam tayi gwanjon motoci 314 da ta kwace

Hukumar hana fasa kwabrin Najeriya watau Kwastam tayi gwanjon motoci 314 da kudinsu ya kai N152 million.

Jawabin da Kakakin hukumar, DCP Joseph Attah, ya saki ya ce an yi gwanjon motocin ne ranar Laraban nan a shafin gwanjon kayayyakin da takeyi mako-mako.

Jawabin ya ce tuni an biya kudin motoci 187 yayinda ake sauraron kudin sauran 127 daga wajen masu saya.

"Tun lokacin da hukumar Kwastam ta bude shafin gwanjon kayayyakin na yanar gizo, mutane da dama sunyi tambayoyi da korafe-korafe, musamman daga wadanda basu samu daman saya ba saboda matsalar lamban kudi haraji NIN, rashin ingantaccen yanar gizo.. kuma hakan ba hurumin hukumar bane."

"Hakazalika wasu sunyi korafin cewa ba'a kwatanta gaskiya wajen shirin gwanjon kayayyaki." Attah yace

"Duk wanda ke shakkan ya yi kokarin duba sunayen wadanda suka samu nasarar saya da bayanansu." Ya kara

Hukumar Kwastam tayi gwanjon motoci 314 da ta kwace
Hukumar Kwastam tayi gwanjon motoci 314 da ta kwace
Asali: Twitter

A bangare guda, Hukumar Yaki da Fatauci da Miyagun Kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta kama katon 607 makare da kwayoyin tramadol guda 11,785,800 a Legas.

Kakakin hukumar NDLEA, Mr Jonah Achema a ranar Laraba 26 ga watan Agusta ne ya bayyana hakan, kuma ya ce shugaban hukumar Muhammad Abdallah ya ce jami'an kwastam sun taimaka wurin kamen.

Abdullah ya ce"An gano wannan ne a cikin wata kwantena mai lamba TCNU 9465832 mallakar wanda ake zargi da laifi da yan sanda suka mika wa hukumar NDLEA.

"Kawo yanzu an gano kwantena 3 da ake yi amfani da su aka boye haramtacciyar kwayar tramadol da wasu kwayoyin da aka shigo da su Najeriya daga kasashen waje."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel