Hukumar NAPTIP ta damke Malamin Islamiyya da laifin lalata yara maza a Kano

Hukumar NAPTIP ta damke Malamin Islamiyya da laifin lalata yara maza a Kano

Hukumar hana safarar mutane ta kasa NAPTIP ta damke wani Malamin makarantar mazauni Unguwar Kadawa, dake karamar hukumar Bunkure a jihar Kano, kan laifin lalata kananan yara maza biyu.

A hirar wayan tarho da wakilin HumAngle yayi da ta kakakin hukumar NAPTIP, Aliyu Abba, ya tabbatar da hakan ranar Juma'a.

Hukumar ta samu labarin cewa Malamin makarantan mai suna Mohammed ya yi luwadi da dalibansa biyu a Unguwar Kadawa, Kwanar Dillalai.

"Yayinda muka samu labarin, mun bazama aiki, mun ceci yaran kuma mun damke mutumin," Abba yace.

A cewar Kakakin NAPTIP, Mohammed ya nada aure kuma ya kasance Malamin Isalmiyya na tsawon shekaru bakwai yanzu.

"Bincike na cigaba da gudana kuma idan aka kammala, za'a gurfanar da shi a kotu," shugaban sashen hukumar na Kano, Shehu Umar ya bayyana.

Ya yi kira ga daukacin al'umma musamman iyaye, da su tabbatar suna leka yaransu dake makarantun allo domin sanin halin da suke ciki.

KU KARANTA: Yan bindiga sun sace dan sanda, jami'in NSCDC tare da wasu mutum jihar Kaduna

Hukumar NAPTIP ta damke Malamin Islamiyya da lalata yara maza a Kano
Hukumar NAPTIP ta damke Malamin Islamiyya da lalata yara maza a Kano
Asali: UGC

Hakazalika hukumar ta ceci wasu mutane shida da akayi safararsu kuma an damke mutum daya.

Ya ce hukumar ta samu labarin yadda ake kokarin safarar mutanen ne a ranar Lahadi, 23 ga Agusta, 2020.

"Hukumar ta kai simame wani Otal mai suna New Paradise Hotel dake Sabon Gari, inda aka damke mai laifin kuma aka ceci mutanen." Umar yace.

"Mutanen sun zo daga jihohin Abia, Oyo, Ogun da Imo ne."

Ya yi bayanin cewa an ajiyesu a dakin Otal din ne domin tafiya da su kasar Libya daga Kano.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel