Buhari ya yi sabbin naɗe-naɗe biyu a NAIC
- Shugaba Buhari ya yi sabbin naɗi guda biyu a NAIC
- Ya naɗa Bashir Babajo a matsayin babban direktan sashin ayyuka na NAIC
- Ya kuma sabunta naɗin Ashinze a matsayin shugaban sashin kuɗi na NAIC
Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Bashir Tijjani Babajo a matsayin direktan sashin ayyuka na hukumar inshoran manoma ta Najeriya, NAIC, karo na farko na shekaru huɗu.
Leadership ta ruwaito cewa shugaban kasar ya kuma sabunta naɗin Philip Ashinze a matsayin babban direktan sashin kuɗi da mulki na hukumar karo na biyu.
Legit.ng ta gano cewa naɗe-naɗen za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Agustan shekarar 2020.

Asali: Twitter
Sanarwar da direktan watsa labarai na ma'aikatar noma da cigaban karkara, Theodore Ogasziechi ya raba wa manema labarai ta ce shugaban kasar ya sanar da amincewarsa na cikin wasikar da ya aike wa ministan Noma, Muhammad Sabo Nanono mai lamba SH/COS/42/3/A/988 mai ɗauke da sa hannun shugaban ma'aikatar fadan shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari.
DUBA WANNAN: Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya sabunta naɗin Ugbo da wasu mutum biyu a NDPHC
Da ya ke taya wadanda aka yi wa nadin murna, ministan ya yi kira garesu su yi amfani da kwarewarsu ta aiki domin cigaba da aiwatar da tsare tsaren NAIC bisa doka da oda.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ce ta mallaki NAIC, kuma an kafa ta ne domin bawa manoman Najeriya inshora.
A wani labarin daban, Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban ƙasa ya amince da nadin Kwanel Dixion Dikio (murabus) a matsayin shugaban riko na shirin yin afuwa ga masu tayar da ƙayan baya.
An ruwaito cewa mai magana da yawun shugaba kasa Buhari, Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar a dandalin sada zumunta ta Twitter a ranar Alhamis 27 ga watan Agusta.
A wani rahoton mai alaƙa da wannan, shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin kwamitin masu zartarwa ta hukumar mutane masu bukata ta musamman, PWD.
Shugaban kasar ya naɗa Hussaini Suleiman Kangiwa a matsayin shugaba sannan ya naɗa James David Lalu a matsayin sakataren kungiyar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng