Yan jarida sun ƙi hallartar taron manema labaran da Fani-Kayode ya kira

Yan jarida sun ƙi hallartar taron manema labaran da Fani-Kayode ya kira

Kungiyar Ƴan Jarida ta Najeriya, NUJ, reshen jihar Akwai Ibom ta umurci ƴaƴanta su ƙauracewa taron manema labaran da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya kira a jihar.

Wannan na zuwa ne kwanaki bayan bullar bidiyon tsohon ministan yana zagin ɗan jaridar Daily Trust, Eyo Charles saboda ya masa tambaya.

Eyo ya tambayi ministan cewa wanene ke ɗaukar ɗawainiyar tafiye-tafiyen da ya yi zuwa jihohin PDP. A martaninsa, Fani-Kayode ya riƙa fada masa kalaman wulaƙanci.

Yan jarida sun ƙi hallartar taron manema labaran da Fani-Kayode ya kira
Yan jarida sun ƙi hallartar taron manema labaran da Fani-Kayode ya kira
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku (Hotuna)

Da farko dai tsohon ministan ya ce bai zai bawa kowa haƙuri ba amma daga bisani ya nemi afkuwar 'abokansa da ke aiki a kafafen watsa labarai.'

Duk da cewa akwai yiwuwar an yafe masa har yanzu dai lamarin yana yi wa wasu ƴan jarida da dama ciwo a zuciyarsu.

Sakamakon haka ne, ƙungiyar ta NUJ, reshen jihar Akwai Ibom a ranar Juma'a ta umurci mambobinta su ƙaurace wa taron manema labaran da Femi ya shirya yi.

A cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a, ƙungiyar reshen ta Akwa Ibom ta ce kada wani ɗan jarida ya hallarci wani taro da tsohon ministan ya shirya.

Ku saurari ƙarin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel