Hotuna: Katin gayyatar ɗaurin auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban ya fito

Hotuna: Katin gayyatar ɗaurin auren Hanan Buhari da Turad Sha'aban ya fito

Katin auren 'yar autan Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan da Turad Sha’aban ya fito.

Za a daura auren ne a ranar Juma'a 4 ga watan Satumbar shekarar 2020 misalin karfe 2 na rana.

Ana sa ran za a daura auren ne a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke babban birnin tarayya Abuja.

Wannan shine daurin aure na farko da za a daura a fadar shugaban kasar ta Aso Rock.

Angon dan tsohon dan majalisa ne, Alhaji Mahmud Sani Sha'aban da ya wakilci mazabar Zaria a Majalisar Wakilai ta Tarayya daga Mayun 2003 zuwa Mayun 2007.

Sha'aban kuma tsohon dan takarar gwamna ne a jihar Kaduna a karkashin tsohuwar jami'yyar Action Congress of Nigeria wato ACN.

Kazalika, Alhaji Mahmud Sani Sha'aban ne wakilin Tudun Wadan Zazzau.

Ba za ayi taro irin yadda aka saba ba na bikin aure duba da cewa har yanzu akwai annobar korona a kasar a cewar katin gayyatar hakan na nufin ba mutane da yawa za su hallarci daurin auren ba.

Ga dai katin gayyatan auren nan a kasa kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban
An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban. Hoto daga LIB
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Bidiyo da Hotuna: Ƴar Indimi ta auri biloniyan ɗan sarki, Malik Ado-Ibrahim

An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban
An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban. Hoto daga LIB
Source: Twitter

An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban
An fitar da katin gayyatar daurin auren Hanan Buhari da Turad Sha’aban
Source: UGC

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel