Dan shugaban Mali da aka hambarar ya tsere kasar waje

Dan shugaban Mali da aka hambarar ya tsere kasar waje

Karim Keita, ɗan hamɓararren Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita da wasu ke jin haushin irin salon rayuwarsa ya tsere daga Mali kamar yadda wata majiya ta shaida wa AFB a ranar Alhamis.

"Ya bar Mali kwanaki biyu da suka shuɗe a mota," in ji wani ɗan majalisa na kusa da Karim da ya kasance a majalisar tun 2013 kuma ya zarce watanni uku da suka wuce.

"Ya kira ni. Lafiyarsa ƙalau," in ji majiyar da ta nemi a sakayya sunan ta.

An kama shugaban ƙasar ne tare da wasu manyan jami'an gwamnati yayin juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar a ranar 18 ga watan Agusta amma Karim ya ɓace ba a kama shi ba.

Wasu hotuna da aka fitar daga wani faifan bidiyo da ke nuna Keita yana rawa da ƴan mata - wadanda majiyar Legit.ng ba ta tabbatar da sahihancinsu ba na cikin dalilan da suka harzuƙa mutan ƙasar.

Ana yi wa ɗan shugaban ƙasar kallon mutum mara cikakken tarbiyya da ke 'cin duniyar sa da tsinke' a yayin da mazauna kasar ke rayuwa cikin talauci da yunwa.

Koken al'umma ya tursasa wa Karin yin murabus na watan Yuli daga matsayinsa na shugaban kwamitin tsaro na majalisar ƙasar duk da cewa ya cigaba da zama ɗan majalisa.

Ɗan majalisar ya ce Karim yana Burkina Faso ko kuma Ivory Coast yayin da wani daga iyalan Keita ya ce ba Morocco ya tafi ba.

"Sojoji sun zo sun kama masu tsaronsa daga nan muka gane cewa yana cikin hatsari. Ya bar ƙasar tun kwanaki biyu," in ji majiyar.

Wata majiya daga jakadojin Afirka ta tabbatar wa AFP cewa Karim yana ɗaya daga cikin kasashen da ke makwabtaka da Mali.

A ranar Alhamis ne sojojin da suka yi juyin mulki suka sako mahaifinsa mai shekaru 75 a yayin da ake cigaba da tattaunawa tsakaninsu da wasu kungiyoyi irinsu Ecowas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel