Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 akan iyakar Najeriya da Kamaru

Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 akan iyakar Najeriya da Kamaru

- Mayakan Boko Haram sun kashe mutum 14 a wani tsuburi dake kan iyakar Najeriya da kasar Kamaru

- Sun kashe mutanen ne sakamakon hana shiga da kayan abinci da mutanen garin suka yi, inda mayakan ke ganin hakan a matsayin cin amana

- A kwana-kwanan dai rundunar sojin sama ta kaiwa mayakan hare-hare da dama ta sama inda tayi sanadiyyar mutuwar da dama daga cikinsu

'Yan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane 14 a wani tsuburi na kasar Kamaru dake Tafkin Chadi kusa da iyakar Najeriya, bayan garin dake kan tsuburin sunyi kokarin hana shigarwa da 'yan ta'addar kayan abinci, cewar wata majiya a ranar Alhamis.

Mayakan sun sauka a tsuburin na Bulgaram akan jirgin ruwa a ranar Talata, kamar yadda rahotanni ya nuna.

Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 akan iyakar Najeriya da Kamaru
Da dumi-dumi: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 14 akan iyakar Najeriya da Kamaru
Source: Depositphotos

"Sun isa wajen da misalin karfe 6:30 na yamma yayin da mutane suke shirin sallar Magariba, sun kashe mutane 14 daga cikin mutanen garin," cewar majiyarta hukumomin tsaro ta sanar da AFP.

Wasu daga cikin wadanda suka mutun an harbe su har cikin gidajensu, yayin da wasu kuma aka kashe su a cikin Masallaci, inda suka je yin sallah, cewar wata majiyar da ta bayyana labarin iri daya.

Sun kai harin gari, inda yake shine babbar hanyar da ake shigarwa da 'yan ta'addar abinci, sai suka yanke shawarar dakatar da shigar da kayan abincin ga mayakan.

KU KARANTA: Duk Bafulatanin da ya shigo jihar Benue a matsayin dan sakai sai mun aika shi gidan yari - Gwamna Ortom

A kwanakin baya, wani babba a garin yayi Yasin da tsinuwa akan duk wani dan garin da yake da hannu wajen shigarwa da 'yan ta'addar kayan abinci.

Mayakan sun dauki hakan a matsayin cin amana, da kuma nuna goyon baya ga jami'an tsaro.

A makonnin da suka gabata sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare da dama kan mayakan inda yayi sanadiyyar mutuwar da yawa daga cikinsu, kamar yadda wata majiya daga gidan sojin ta bayyanawa manema labarai.

"Mayakan sun yadda cewa hana shigar da kayan abincin na daya daga cikin hanyoyin da sojojin suke son bi wajen kashe su da yunwa, yayin da kuma suke yi musu ruwan bama-bama ta sama," cewar majiyar.

Yankin Tafkin Chadi dai yana daga cikin wajen da Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi suke rabawa.

Yammacin wannan tafki ya zama sansanin 'yan ta'addar dake Najeriya, wadanda suka shafe shekara goma suna abu daya, sun kuma yi sanadiyyar rasa dubunnan rayuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel