Batanci ga Annabi: A shirye na ke in rattaba hannu kan hukuncin kisa da kotu ta yanke - Ganduje

Batanci ga Annabi: A shirye na ke in rattaba hannu kan hukuncin kisa da kotu ta yanke - Ganduje

Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis ya ce a shirye ya ke ya saka hannu domin a zartar da hukuncin kisar da kotu ta yanke wa mawaƙi Yahaya Sharif-Aminu da ya yi ɓatanci ga Manzon Allah (SAW).

Idan za a iya tunawa babban kotun Shari'a da ke Kano ta samu Aminu-Shariff da laifin batanci kuma ya yanke masa hukumcin kisa ta hanyar rataya.

A watan Maris ɗin shekarar 2020, mawaƙin mai shekaru 22 ya rera wata waƙa mai ɗauke da batanci ga Manzon Allah ya tura a dandalin sada zumunta ta WhatsApp, hakan ya sa mutane suka harzuƙa.

Batanci ga Annabi: A shirye na ke in rattaba hannu kan hukuncin kisa da kotu ta yanke - Ganduje
Batanci ga Annabi: A shirye na ke in rattaba hannu kan hukuncin kisa da kotu ta yanke - Ganduje. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

Da ya ke jawabi bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Alhamis, Ganduje ya ce kotu ta bawa wanda aka yanke wa hukuncin wa'adin kwanaki 30 don ɗaukaka ƙara, idan bai ɗaukaka karar ba shi kuma ba zai bata lokaci wurin rattaba hannu a kan hukuncin ba.

DUBA WANNAN: Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku (Hotuna)

Ya ƙara da cewa, "idan kuma wanda aka yanke wa hukuncin ya ɗaukaka ƙara, za mu jira mu bi Shari'ar har zuwa kotun daukaka ƙara. Idan ya sake ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli, zamu tafi can.

"Idan kotun ƙoli ta jadadda hukuncin da ƙananan kotun suka yanke, gwamnan jihar Kano ba zai ƙara ko minti guda ba zai saka hannu a kan dokar aiwatar da kisar," a cewar Ganduje.

Ganduje ya kuma koka a kan yadda ake ƙara samun yawaitar kalaman ɓatanci a ƴan kwanakin nan, ya ce gwamanti ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba har sai ta magance matsalar.

Gwamna Ganduje ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi na tabbatar da doka da oda a jihar.

A jawabin da suka yi, malaman addinin musulunci da dama sun nuna goyon bayansu ga hukuncin kisar da kotun ta yanke, inda suka ce wannan itace hukuncin da ya dace ga duk wanda ya zagi Annabi.

Malamin sun shawarci gwamnan ya yi watsi da ƙungiyoyin kare hakkin bil adama da ke son yin katsalandan a lamarin inda suka ce addinin musulunci ya riga ya tanadi hukunci ga wanda ya zagi Manzon Allah.

Daya daga cikin malaman, Usman Makwarari ya bayar da shawarar cewa a zartar da hukuncin kisar a bainar jama'a saboda ya zama darasi ga sauran mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel