Bamu amince Ganduje ya karbi bashi daga wajen China ba - Dattawan Kano sun kaiwa Buhari kara

Bamu amince Ganduje ya karbi bashi daga wajen China ba - Dattawan Kano sun kaiwa Buhari kara

Wata kungiyar mai sunan gamayyar dattawan Kano ta kai karan gwamnan jihar Kano wajen shugaban kasa, Muhammadu Buhari, majalisar dattawa, da ma'aikatar kudin tarayya kan bashin bilyan 300 da yake shirin karbowa daga kasar Sin.

Kungiyar dake karkashin jagorancin tsohon dan takaran shugaban kasan Najeriya karkashin jam'iyyar National Republican Convention (NRC), Alhaji Bashir Tofa, ta bayyana rashin amincewarta da kafewan da gwamna Ganduje yake yi na karbo bashi daga bankin cigaban kasar Sin don gina layin dogon a cikin birnin Kano.

Alhaji Bashir Tofa, a takardar da rattafa hannu, ya ce sabanin wasu yan tsiraru da suka san sharrudan da kasar Sin ta bada don bayar da bashin, babu wanda ya sani kuma ana rufa-rufa da ka'idojin.

Bashin kudin gina layin dogo: Dattawan Kano sun kai karan Ganduje wajen Buhari
Bashin kudin gina layin dogo: Dattawan Kano sun kai karan Ganduje wajen Buhari
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari ya bada umurnin kada farashin wutan lantarki, amma ba zai shafi talaka ba - NERC

Jawabin yace: "Shafin farko na aiki zai ci bilyan 300, ko bilyan 828 kamar yadda wasu ke fada, kuma ace daga wasu yan kasar waje abin damuwa ne. Ya zama wajibi a sake tunani."

"Bisa alkaluman da ofishin kula da basussukan DMO ta bayar kan basussukan dake kan jihar Kano, da matukar wuya jihar Kano ta iya biya idan ta karbi wani bashi yanzu."

"Ya kamata a sani cewa aikin layin dogo ba abu bane da za'ayi gaggawan yi saboda ko ita gwamnatin jihar ba tayi lissafin yi yanzu ko da dadewa ba."

"Idan kasar Sin da gaske na son taimaka mana da bashi mai sauki, toh a a taimaka a bangarori masu muhimmanci irin ilimi, kiwon lafiya, aikin noma, kimiya da fasaha, ayyuka, masana'antu da ruwan sha."

A ranar 28 ga watan Yuli, Legit HAusa ta kawo muku rahoton cewa gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa babu ja da baya wajen niyyar karban bashi don gina layin dogon jirgin kasa a cikin garin Kano, wanda aka yanke bayan neman shawari daga masu ruwa da tsaki a jihar.

Gwamnatin jihar ta jaddada cewa an shirya ginin layin dogon ne domin fadada harkokin kasuwanci a jihar da saukake sufuri don amfanin gona a jihar.

ThisDay ta ruwaito cewa kwamishanan labaran jihar, Muhammad Garba, ya saki takarda a daren Litnin domin martani ga Kwankwasiyya kan aikin.

Ya ce babu irin sukan da zai hana gwamnatin jihar aiwatar da manyan ayyuka don mayar da jihar Kano babbar birni.

Garba ya ce tun da bankin shiga da ficen kasar China ya amince da baiwa jihar bashin, gwamnatin jihar ba zata bata lokaci ba wajen kaddamar da ginin da za'a fara daga kasuwan kayan hatsi dake Dawanau zuwa Bata.

Ya ce an bi dukkan ka'idojin da ya kamata, wanda ya hada da sa hannun majalisar dokokin jihar, majalisar dokokin tarayya da wasu manyan ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel