Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku (Hotuna)

Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku (Hotuna)

An yanke hukuncin zaman gidan yari na har abada a kan ɗan ta'adda mai shekaru 29, Brenton Tarrant da ya kashe musulmi 51 a wani masallaci da ke New Zealand.

Wannan hukuncin shine irinsa na farko da aka fara yanke wa wani a kotun ƙasar a ranar Alhamis 27 ga watan Agusta bayan Tarrant ya amsa laifinsa a farkon wannan shekarar.

Ya amsa cewa ya yi wa mutane 51 da suka hada mata, maza da ƙananan yara kisar gilla a wani masallaci a ranar 15 ga watan Maris na shekarar 2015.

Cikin wadanda ya kashe har da yaro mai shekaru 3 kacal a duniya.

A ranar 15 ga watan Maris, Tarrant ya yi tafiya a motarsa na awa hudu da rabi daga Dunedin zuwa Christchurch kimanin nisar kilomita 360.

Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku
Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

Misalin ƙarfe 1.30 na rana a ranar a lokacin da masallata ke ibadansu na ranar Juma'a, Tarrant ya sanar da ƴan uwansa abinda ya yi shirin aikatawa.

Daga nan kuma sai ya kunna bidiyo na kai tsaye da dandalin sada zumunta ta Facebook ya tafi masallacin Al Noor inda ya kashe mutum 44 ya kuma ta raunata 35.

Daga nan kuma ya tafi Linwood Islamic Centre inda ya kashe wasu mutum bakwai ya kuma raunatta wasu biyar.

Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku
Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

A kan hanyarsa ta komawa motarsa don ya ƙara ɗibo makamai ne wani Abdul Aziz Wahabazadah ya kore shi ya harbe shi da na'urar POS a kai sannan ya fasa masa gilashin mota da bindigarsa.

Yana hanyarsa na zuwa wuri na uku da zai yi kisar ne ƴan sanda suka tsare shi suka kama shi.

Tarrant ne mutum na farko da aka taba samu da laifin ta'addanci kuma ya amsa dukkan tuhume-tuhume 40 da aka masa na yunkurin kisa da ta'addanci.

Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku
Dan ta'addan da ya bindige musulmi 51 cikin masallaci zai ƙare rayuwarsa a kurkuku. Hoto daga LIB
Asali: Twitter

An soke hukuncin kisa a New Zealand a 1961 saboda haka ba za a iya yanke masa hukuncin kisa ba sai dai na zaman kurkuku na har abada ba tare da yiwuwar saƙinsa ba.

Mai shari'a, Cameron Mander, yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis ya tambayi Tarrant ko yana da abin cewa sai ya ce, "A'a, nagode,".

Mai Shari'a Mander ya karanto dukkan sunayen waɗanda Tarrant ya kashe tare da irin illar da ya yi musu.

"Ba ka da tausayi. Abinda da ka aikata zalunci ne da rashin jin ƙai," Mander ya faɗa wa Tarrant.

Farai Ministan ƙasar Jacinda Ardern ta nuna gamsuwarta da hukuncin da aka yanke masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel