Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi

Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi

- Wai an ce tsautsayi ba a saka maka raana, wannan magana haka take, domin kuwa West Mathewson bai taba tunanin haka za ta faru da shi ba

- Mathewson wanda yake kiwon wasu fararen zakuna mata masu kyau, ya rasa ransa sakamakon hari da suka kai masa a lokacin da yake wasa da su

- Bayan kai masa harin an garzaya da shi asibiti, sai dai kuma kafin su kai asibitin rai yayi halinsa

Wani mutumi da ya dauki soyayyar duniya ya dorawa wasu zakuna guda biyu da ya raina tun suna yara sun kashe shi cikin yanayi na rashin kyawun gani.

Mutumin mai suna West Mathewson, mai shekaru 68, yana tsakiyar wasa da zakunan nashi masu suna Demi da Tanner a ranar Laraba 26 ga watan Agusta, sai kawai daya daga cikinsu ta taso mishi.

Matarshi Gill, mai shekaru 65, tayi kokarin ceto mijin nata, inda tayi kokarin janye hankalin zakunan, amma ina tuni har sun ji masa mummunan rauni.

Ya mutu sakamakon wannan ciwo da suka ji mishi a yayin da ake kan hanyar kai shi asibiti.

Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi
Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi
Asali: Facebook

Wannan dai ba shine karo na farko da zakunan suka kashe mutum ba. A shekarar 2017, sun kashe wani ma'aikacin gona da yake aiki a gonar Mr Mathewson, dake Hoedspruit kusa da wajen shakatawa na kasar Afrika ta Kudu.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja

Duk da haka amma, West Mathewson ya cigaba da wasa da su kullum, inda ya yadda cewa baza su taba kai masa hari ba.

Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi
Abu kamar wasa: Zakuna sun cinye mutumin da ya raine su tun suna yara a lokacin da suke wasa da shi
Asali: Facebook

An bayyana cewa West yana son wadannan zakuna kamar yadda yake son 'ya'yan cikinsa, saboda yana zama dasu a koda yaushe yana wasa da su kullum.

An bayyana cewa zakuna basu yi niyyar cutar da shi ba, kawai dai kuskurene aka samu.

Duk da wannan lamari da ya faru, mutane da yawa da suka je wajen yawon bude ido sun cigaba da yawo da dabbobin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel