Yadda aka kama babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a ofis a lokacin da yake ganawa da abokanan aikinshi a kiran bidiyo na zoom

Yadda aka kama babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a ofis a lokacin da yake ganawa da abokanan aikinshi a kiran bidiyo na zoom

- Asirin wani babban ma'aikacin gwamnati a kasar Philippine ya tonu, bayan an kama shi yana lalata da sakatariyar shi

- Mutumin dai ya fara taron kiran bidiyo a manhajar Zoom ke da wuya sai ya koma yana lalata da sakatariyar tashi bai san cewa kowa na gani ba

- Bayan sun kammala ya dawo ya cigaba da ganawa da abokanan aikinshi kamar babu abinda ya faru

An kama wani babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a cikin ofis a lokacin da rashin sani ya sanya ya fara kiran waya na bidiyo da abokanan aikin shi a kasar Philippines.

Kamar yadda rahoto ya nuna, ma'aikata daga garin Fatima Dos dake Cavite suna gabatar da taro ta manhajar zoom kamar yadda suka saba a ranar Laraba.

Shugabansu Jesus Estil, wanda aka bayyana cewa bashi da ilimi akan harkokin na'ura mai kwakwalwa yaje ya danna wani wuri sai kyamarar na'urarshi ta fara aiki.

Yadda aka kama babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a ofis a lokacin da yake ganawa da abokanan aikinshi a kiran bidiyo na zoom
Yadda aka kama babban jami'in gwamnati yana lalata da sakatariyarshi a ofis a lokacin da yake ganawa da abokanan aikinshi a kiran bidiyo na zoom
Asali: Facebook

Bayan sun fara taron, shugaban nasu ya tashi daga kan kujerarshi ya tinkari wata mata dake zaune a can gefe, bayan dakiku kadan, kawai sai gani aka yi sun fara lalata yayin da sauran abokanan aikinshi suke kallo.

Daga baya shugaban da matar sun dawo sun cigaba da halartar taron basu san cewa asirinsu ya tonu ba.

KU KARANTA: Naira miliyan 1 aka bamu aka ce muyi mata fyade mu kasheta - Cewar wadanda suka kashe Uwaila

Daga baya an gano cewa wannan matar ashe sakatariyar shi ce, wacce kuma ita ce ke kula da harkar kudi a ofishinsa.

Bidiyon wanda daya daga cikin ma'aikatan ya dauka, an wallafa shi a shafukan sadarwa, inda hakan ya jawo mutanen garin suka bukaci a cire mutumin daga mukaminsa.

Ma'aikatar cikin gida da kananan hukumomi ta tabbatar da cewa za a kori Estil daga kan mukaminsa cikin gaggawa.

Shugaban ma'aikatar Cif Richard Geronimo, ya ce: "Wannan ba karamin laifi bane, babban laifi ne. Zamu yi iya bakin kokarinmu wajen hukunta shi."

Estil dai ya bukaci a yafe masa, amma ina hakan bai yiwu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng