Mutum 16 sun mutu yayin da babbar mota ta murƙushe ƙananan motocci 3 a Zamfara

Mutum 16 sun mutu yayin da babbar mota ta murƙushe ƙananan motocci 3 a Zamfara

- Mutane 16 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hatsari da ya faru a Zamfara

- Hatsarin ya faru ne yayin da wata babbar mota ta kwace wa direba ta bi ta kan ƙananan motocci uku

- Tuni dai an kwashe gawarwakin wadanda suka rasu kuma daga bisani aka yi jana'izar su a asibitin Ƙwararru ta Yariman Bakura a Gusau

A ƙalla mutane 16 ne suka riga mu gidan gaskiya kuma wasu da dama suka jikkata yayin da mota ta kashe wa wani direban babbar mota ya bi ta kan wasu motocci uku a Zamfara.

Hadarin ya faru ne yayin da ake yayyafi a yammacin ranar Laraba kusa da garin Fegin Ɗan Marks da ke hanyar Funtua zuwa Gusau.

Mutum 16 sun mutu yayin da babbar mota ta murƙushe ƙananan motocci 3 a Zamfara
Mutum 16 sun mutu yayin da babbar mota ta murƙushe ƙananan motocci 3 a Zamfara
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An naɗa ɗan Najeriya Ministan Shari'a a Canada (Hotuna)

Lamarin ya faru ne jim kadan bayan gwamnan jihar, Dakta Bello Mohammed Matawalle ya wuce a kan hanyarsa ta koma wa gida bayan ziyarar da ya kai wa Shugaba Buhari a Abuja.

Gwamna Matawalle ya samu labarin hadarin kafin ya isa Gusau hakan yasa ya juyo nan take ya iso inda abin ya faru ya umurci a kai gawarwakin asibitin kwararru ta Yariman Bakura da ke Gusau.

Gwamnan ya bayar da umurnin a tuntubi ƴan uwan wadanda hadarin ya ritsa da su kuma ya bukaci ma'aikatan asibitin su taho aiki da wuri domin a yiwa wadanda suka rasu jana'iza a goben ranar.

Tuni dai an yi wa wadanda suka rasun jana'iza.

Mai magana da yawun hukumar kiyayye haɗɗura ta ƙasa, FRSC, reshen jihar Zamfara, Mista Yassar Shehu ya tabbatar da afkuwar hadarin.

Ya ce gudu fiye da kima da obatekin ba bisa ƙa'ida ba ne suka janyo hatsarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164