Da duminsa: Sojin Mali sun sanar da sakin shugaba Boubacar Keita

Da duminsa: Sojin Mali sun sanar da sakin shugaba Boubacar Keita

Sojin kasar Mali da suka hambarar da mulkin shugaban kasa Boubacar Keita, sun sanar da sakinsa a yau Alhamis.

Shugabannin mulkin sojin sun damke shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita tun a ranar 18 ga watan Augustan 2020.

Dakarun sojin, wadanda suke kiran kansu da kwamitin ceton jama'a na kasa, sun sanar da hakan a kafar sada zumuntar zamani na Facebook.

Sun ce, "Muna sanar da gida da kasashen ketare cewa mun sako tsohon shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita. A halin yanzu yana gidansa".

An sako Keita ne bayan bukatar da kasashe masu makwabtaka da Mali da kungiyoyin duniya suka mika musu.

Da duminsa: Sojin Mali sun sanar da sakin shugaba Boubacar Keita
Da duminsa: Sojin Mali sun sanar da sakin shugaba Boubacar Keita. Hoto daga Channels TV
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Sojin Mali sun sanar da sakin shugaba Boubacar Keita

A wani labari na daban, kungiyar hadin kan kasashen Afrika na yamma, sun kushe abinda ya faru a kasar Mali tare da daukar alkawarin ladabtarwa wanda ya hada da tara.

Sojojin adawa sun kama shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita da firayim minista Boubou Cisse a ranar Talata, bayan makonni da aka kwashe ana rikicin siyasa a kasar.

Lamarin ya ci gaba inda sojojin suka kwace babban barikin sojin da ke babban birnin Bamako da safiyar ranar.

A wata takarda da ECOWAS ta aike musu, ta ce dukkan kasashen Afrika ta yamma za su rufe iyakokin da ke tsakaninsu da Mali na kasa da na sama kuma za ta ci tararsu.

Kungiyar kasashen 15 wanda ya hada da Mali, ta kara da cewa za ta dakatar da kasar daga cikin masu yanke hukuncinta.

"ECOWAS cike da jimami ta gano yadda sojin kasar Mali suka kwace mulki," takardar ta ce, wacce aka wallafa da harshen Faransanci.

Mali ta kasance tsundum cikin rikicin siyasa tun a watan Yuni inda aka dinga bukatar Shugaban kasa Keita ya yi murabus.

A ranar 5 ga watan Yuni ne 'yan adawar suka fito domin zanga-zanga tare da nuna fushinsu a kan lalacewar tattalin arzikin, rashawa a gwamnati da kuma ta'addanci.

Kungiyar adawar ta ci gaba da zanga-zanga inda a watan jiya har rayukan mutane 11 suka salwanta a cikin kwanaki uku bayan rikicin da ya barke.

A kokarin dakile rikicin, ECOWAS ta shiga lamarin domin yin sasanci. Kungiyar ta yanke shawarar hada gwamnatin hadin kai da sauran matakai a watan da ya gabata, amma Keita ya soki hakan.

Zanga-zangar ranar 5 ga watan Yuni ta ci gaba da tada hankali tare da assasa cewa sai Keita ya sauka daga mulkin kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel