Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa

Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa

A kokarin ta na kawo karshen kallubalen rashin tsaron da ake fama da shi a Arewa maso Tsakiya, Dakarun soji na musamman ta Operation Whirl Stroke sun samu gaggarumin nasara a kan bata gari.

A wani harin da sojojin na Operation Whirl Stroke suka kai duk dai a garin na Uttu a ranar 26 ga watan Agustan 2020 sun gano wata kamfanin kera bama bamai mallakar kungiyar Darul Salam.

Sojojin sun gano wannan wurin ne sakamakon bayyanan sirri da aka samu daga hannun mutane da kuma amfani da fasaha ta zamani.

Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa
Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mutum mai shekaru 50 ya mutu cikin rijiya a Kano

Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa
Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa
Asali: Twitter

A yayin harin, sojojin sun kwato kayayyakin hada bama bamai da abubuwa masu fashewa da dama da suka hada da buhun taki, rabin buhun hodar bindiga, gurneti na hannu 10, naurar kunna gurneti, naurar harba roka da wasu muggan makamai.

Sojojin sun yi fatafata da sansanin kuma sun bazama cikin dajin domin bin sahun yan taadan kungiyar da suka tsere.

Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa
Hotuna: An gano wurin ajiyar makaman 'yan ta'adda a Nasarawa
Asali: Twitter

Bayan wasu hare hare da sojojin suka kai a mabuyar yan bindiga, a kalla mutum 410 ne cikin 'yan kungiyar ta'adanci ta Darul Salam ciki har da mata da yara suka mika wuya ga sojojin na Whirl Stroke da sauran jamian tsaro a Uttu na karamar hukumar Toto na jihar Nasarawa.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Agusta kamar yadda sanarwar da hukumar soji ta fitar da shafinta na Twitter mai lakabin @DefenceInfoNG

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel