Da duminsa: Shugaba Buhari na jagorantar zaman dukkan shugabannin yau da jiya na Najeriya

Da duminsa: Shugaba Buhari na jagorantar zaman dukkan shugabannin yau da jiya na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na jagorantar zaman dukkan masu ruwa da tsaki a harkar Najeriya na yau da jiya a fadar shugaban kasa dake AsoVilla, Abuja.

An fara zaman ne misalin karfe 11 na safe kuma tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, kadai ne tsohon shugaban kasan dake hallare a wajen, The Nation ta ruwaito.

Sauran tsaffin shugabannin kasan sun hallara ta yanar gizo.

Daga cikinsu akwai tsohon shugaban mulkin Soja, Ibrahim Badamasi babangida,; Cif Ernest Shonekan; da Janar AbdusSalam Abubakar.

Daga cikin wadanda ke wajen mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbaji (SAN), shugaban majalisar dattijai, Ahmed Lawan; Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; da kuma shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Hakazalika akwai wasu tsaffin manyan Alkalan tarayya da suka hallara.

Daga cikin ministocin Buhari dake wajen kuwa, akwai Ministan Shari'a, Abubakar Malami da MInistan birnin tarayya, Mallam Muhammad Bello.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel