Yadda ƴan Boko Haram suka yanka Dattawan Borno 75 a dare ɗaya - Sanata Ndume

Yadda ƴan Boko Haram suka yanka Dattawan Borno 75 a dare ɗaya - Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume bayar da labarin yadda ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram suka yi wa dattawa 75 a Borno yankan rago a cikin dare ɗaya.

Ndume ya bayyana hakan ne wurin taron da kwamitin majalisar dattawa na ayyuka na musamman da arewa maso gabas ta shirya a Maiduguri a ranar Laraba 26 ga watan Agusta.

Sanata mai wakiltar yankin Borno ta Kudu ya ce kafafen watsa labarai ba su wallafa abubuwan da ke faruwa a yankin kamar yadda ya kamata.

Yadda ƴan Boko Haram suka kashe Dattawan Borno 75 a dare ɗaya - Sanata Ndume
Yadda ƴan Boko Haram suka kashe Dattawan Borno 75 a dare ɗaya - Sanata Ndume
Asali: UGC

Ndume ya ce ko a matsayinsa na sanata ba zai iya zuwa garinsu na Gwoza ba saboda babu tsaro. Ya kuma bayar da labarin yadda ƴan ta'addan suka tara samari a Gwoza suka harbe su har lahira.

DUBA WANNAN: Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Borno za ta rushe gidaje 1,300

Ya ce;

"Idan da kwamitin majalisar dattawa za ta dauki lokaci da ziyarci sansanin ƴan gudun hijira da ƙaramar hukumar Konduga, za mu fahimci abinda ke faruwa.

"Ko a matsayi na na sanata, ba na iya zuwa garin mu na Gwoza saboda babu tsaro.

"Jami'an tsaron mu suna iya kokarinsu amma abin ya musu yawa. Mutane na mutuwa a kullum saboda hari ko yunwa. Mun rasa mutanen mu da dama a can.

"Akwai wani lokaci a garin mu, Gwoza da ƴan Boko Haram suka kama dattawa kimanin 75 suka kai su mayanka suka yanka su kaman dabbobi. Mutum biyu kawai suka tsira saboda maharan sunyi tsamanin sun mutu ne duba da yadda jinin wasu ya rufe su.

"Duk dai a Gwoza, akwai lokacin da ƴan Boko Haram suka kama matasa masu yawa suka jera su suka harbe har lahira. Wannan kaɗan daga cikin wadanda suka yi ƙaurin suna ne kawai."

Ndume ya kuma ce batun yunwa ya yi sauki ne saboda tallafin da kungiyoyin tallafawa al'umma ke yi a Borno. Ya ƙara da cewa wannan da wasu abubuwan suka sa ya ke ganin akwai bukatar kafa hukuma ta cigaban arewa maso gabas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel