Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya sun bankawa wani matashi harsashi kan ya yiwa wata karamar yarinya ciki

Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya sun bankawa wani matashi harsashi kan ya yiwa wata karamar yarinya ciki

- 'Yan sanda a jihar Ribas sun harbi wani matashin saurayi a kafa bisa kama shi da wani laifi

- 'Yan sandan sun kama shi da laifin yiwa wata yarinya cikin shege, inda suka biyo shi har gidan mahaifinsa suka harbe shi a kafa

- Daga baya 'yan sandan sun dauke shi cikin jini sun wuce da shi zuwa wani asibiti

Wani matashi mai suna, Ledisi Kote, yana kwance yana fama da kanshi a wani asibiti, bayan wasu jami'an 'yan sanda na jihar Ribas sun harbe shi a kafa sakamakon wata yarinya da ya yiwa cikin shege.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa wasu jami'an 'yan sanda dake aiki a Kpor cikin karamar hukumar Gokana a jihar, a ranar Juma'a 21 ga watan Agusta, 2020, sun shiga gidan mahaifin Ledisi dake K. Dere da misalin karfe 7 na safe, inda suka bukaci ganin matashin dan shekara 19.

Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya sun bankawa wani matashi harsashi kan ya yiwa wata karamar yarinya ciki
Tirkashi: 'Yan sandan Najeriya sun bankawa wani matashi harsashi kan ya yiwa wata karamar yarinya ciki
Source: Facebook

An ruwaito cewa 'yan sandan sun shiga dakin Ledisi, suka fito dashi suka harbe shi a kafa.

Wani mai kare hakkin dan Adam, Tuka Loanyie, wanda ya wallafa rubutu game da Ledisi a facebook, ya bayyana cewa 'yan sandan, wadanda suka dauki yaron bayan sun harbe shi sun ajiye shi a wani asibiti a cikin yankin.

Loanyie, wanda ya bukaci abi hakkin matashin, ya bayyana cewa akwai yiwuwar sai an yiwa Ledisi aiki har kusan sau uku a kafa kafin ya samu ya cigaba da tafiya.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun ceto wasu yara kanana guda 2 da aka garkame a cikin bandaki a Abuja

Ya ce; "A cewar mahaifin yaron, yana zaune a tsakar gida sai yaga mota mai kirar Sienna ta shigo wajensu dauke da 'yan sanda guda hudu.

"Suna zuwa suka wuce dakin dan shi, suka shiga. Ya tinkare su yayi tambaya akan abinda dan shi yayi da suke neman shi haka, amma cikinsu babu wanda ya amsa masa tambayarsa. Daga baya daya daga cikinsu cikin fushi ya bayyana masa cewa danshi ya yiwa wata yarinya cikin shege.

"Abu na gaba da ya jiyo shine karar harbin bindiga. Daya daga cikin 'yan sandan ya harbi yaron a kafa, saboda kawai ya yiwa yarinya ciki. Sun dauke shi sun wuce dashi cikin jini, inda suka boye shi a wani asibiti.

"Nayi wannan rubutu ne saboda har yanzu, jami'an da suka yi wannan sunki su dauki nauyin kudin maganin yaron. Likita yace sai anyi masa aiki har sau uku a kafa ko kuma a yanke kafar. Muna son a yiwa yaron nan adalci, zai iya zama ni ko kai gobe."

PUNCH ta gano cewa an kai lamarin zuwa helkwatar 'yan sanda ta jihar Ribas dake Moscow Road, Fatakwal.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel