Kano: An dakatar da mai unguwa saboda safarar kananan yara

Kano: An dakatar da mai unguwa saboda safarar kananan yara

Masarautar jihar Kano ta dakatar da mai unguwan Sabon Gari, Ya'u Muhammad a kan zarginsa da hannu wurin safarar ƙananan yara.

Muhammad Umar, sakataren Galadiman Kano, Abbas Sanusi ne ya fitar da sanarwar hakan a ranar Talata a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, masarautar ta dakatar da dagajin ne har zuwa lokacin da za a kammala bincike da hukumar hana fataucin mutane na ƙasa, NAPTIP, ke yi.

Masarautar Kano ta dakatar da dagaji saboda safarar yara
Masarautar Kano ta dakatar da dagaji saboda safarar yara. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da sabbin nade-nade a hukumomi 9 (Sunaye)

Majiyar Legit.ng Hausa ta ruwaito cewa NAPTIP tana binciken wanda ake zargin ne tare da wani kwamandan Hisbah, Jamilu Yusuf kan zarginsu da hannu wurin sayarwa wata mata ƴar jihar Imo jinjiri.

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, wani mutum mai shekaru 50, Abdulhamid Muhammad ya mutu a cikin rijiya a kauyen Sha’iskawa da ke karamar hukumar Danbatta na jihar Kano a ranar Talata.

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saidu Mohammed ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya rabar wa manema labarai a ranar Talata a Kano.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata a lokacin da marigayin ya shiga rajiyar domin ya ceto tinkiya da ta fada ciki.

Mai magana da yawun hukumar ya ce, "Wata Malama Ummi Muhammad ta kira mu a waya misalin karfe 4.37 na asuba ta lambar mu na ofishin hukumar kiyaye gobara ta Danbatta."

"A lokacin da aka sanar da mu abinda ya faru, mun tura jamian mu cikin gaggawa inda suka isa wurin misalin karfe 4.42 na asuba.

"An ciro gawar Muhammad daga rijiyar sannan aka kai shi Babban Asibitin Danbatta."

Hukumar ta kwana kwana ta shawarci mutane su dena jefa kansu cikin hadari, abinda ya fi dace wa shine su kira layukkan wayar kar ta kwana na hukumar kamar haka: 08107888878, 08098822631, 07051246833, da 07026026400.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel