Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin

Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, a ranar Talata ya ziyarci Magumeri, hedkwatar karamar hukumar Magumeri ta jiharsa bayan harin 'yan Boko Haram.

Gwamnan ya yi jawabi ga mazauna yankin, kuma ya duba yanayin barnar da mayakan ta'addancin suka yi a asibitin Magumeri da ba a dade da gyarawa ba.

A sakon Zulum ga mazauna yankin yayin jawabinsa, ya yi kira ga mazauna yakin da su kai rahoton duk wani mutum ko kaiwa da kawowa da basu yadda da ita ba ga jami'an tsaro don kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci.

Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin
Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin. Hoto daga Gwamna Zulum
Asali: Twitter

"Akwai matukar amfani idan mazauna yankin suka bai wa jami'an tsaro goyon baya ta hanyar samar musu da bayanan sirri, don samun hanyar damko 'yan ta'addan da masu goyon bayansu.

"Bayanai daga jama'ar yankin na da matukar amfani. Baya ga karfafa CJTF, gwamnati na kira ga jama'ar yankin da su samar da bayanai ga dakarun sojin da sauran hukumomin tsaro," Zulum yace.

Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin
Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin. Hoto daga Gwamna Zulum
Asali: Twitter

Zulum ya bai wa ma'aikatar gyara umarni da ta hada kai da ma'aikatar lafiya domin gaggauta gyaran asbitin tare da mayar da dukkan ababen amfanin da mayakan ta'addanci suka tarwatsa.

KU KAARANTA: Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, zai kai ziyara masarautar Ilorin a ranar Alhamis

Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin
Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin. Hoto daga Gwamna Zulum
Asali: Twitter

"Ba za mu yi kasa a guiwa ba wurin kokarin ganin gyaran yankunan tare da dawo da jama'ar yankin. Kwamishinan RRR na jihar ya tabbatar da gaggauta gyaran asibitin.

"Da izinin Allah ba za mu yi kasa a guiwa ba wurin tabbatar da gyaran dukkan kayan more rayuwa da aka lalata a jihar," Zulum yace.

Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin
Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin. Hoto daga Gwamna Zulum
Asali: Twitter

Ya kara da cewa, "Za a tabbatar da samuwar cibiyoyin lafiya masu inganci ,wadanda talakawa za su iya amfana da su. Wannan na daga cikin babban burin gwamnatina.

"Ana kammala gyaran asibitin, za mu mayar da dukkan kayayyakin da aka lalata. Za mu tabbatar da cewa mun samar da ma'aikata isassu a asibitin."

Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin
Harin Magumeri: Zulum ya kai ziyara, ya bada umarnin gaggauta fara gyaran yankin. Hoto daga Gwamna Zulum
Asali: Twitter

Zulum ya tabbatarwa da mazauna Magumeri da cewa za a samar musu da tsaro isasshe ga rayukansu da dukiyoyinsu.

"Gwamnati na tatatunawa da dakarun sojin Najeriya da 'yan sanda don samar da tsaro mai inganci a Magumeri," Zulum yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel