Boko Haram: Ma'aikacin jinya ya kubuta bayan kwashe wata 8 a hannun 'yan ta'adda

Boko Haram: Ma'aikacin jinya ya kubuta bayan kwashe wata 8 a hannun 'yan ta'adda

Wani ma'aikacin jinya dan Najeriya wanda mayakan ISWAP suka yi garkuwa da shi tun farkon shekarar 2020, ya samu tserowa daga hannun 'yan ta'addan.

Dawowar ma'aikacin jinyar, wanda aka kare sunansa da inda yake aiki, ya samu nasara ne sakamakon aiki tukuru na jami'an tsaron hadin guiwa na MNJTF.

Wannan na kunshe ne a wata takardar da Kanal Muhammad Dole, shugaban fannin yada labarai na MNJTF da ke da hedkwata a Ndjamena, babban birnin Chadi ya fitar.

Kanal Dole ya yi bayanin cewa, kungiyar jami'an tsaron na hadin guiwa sun dage wurin sauke nauyin da ya hau kansu na ceto yankunan da ta'addancin yayi kamari.

Kamar yadda yace, ma'aikacin jinyar ya kasance a hannun mayakan ISWAP a yankin tafkin Chadi, daya daga wuraren da 'yan ta'addan suka kama kuma suke walwalarsu.

"Bayan saukar bama-bamai daga jiragen yaki, duk wuraren sun kama da wuta inda 'yan ta'addan da wadanda suka sace suka fara neman tseratar da rayukansu.

"Dole ta sa nayi amfani da dama ta. Ina matukar Godiya ga Ubangiji da ya bani damar tserewa," ma'aikacin jinyar yace.

Boko Haram: Ma'aikacin jinya ta kubuta bayan kwashe wata 8 a hannun 'yan ta'adda
Boko Haram: Ma'aikacin jinya ta kubuta bayan kwashe wata 8 a hannun 'yan ta'adda. Hoto daga Channels TV
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun damke dan fashi yayin da yayi yunkurin yi wa mai takaba fyade a gaban 'ya'yanta

Daga nan ne ma'aikacin jinyar ya samu ya kubuta ya kama hanyar wani kauye a jamhuriyar Nijar kuma ya mika kansa ga jami'an tsaro na hadin guiwa.

Kanal Dole ya bayyana cewa, an dauko ma'aikacin jinyana jirgi inda aka mika shi ga hukumomi a Najeriya wadanda suka fara da duba lafiyarsa kafin komai.

Sun gaggauta duba lafiyarsa ne kuwa sakamakkon sanar da su da yayi cewa ya kwashe watanni takwas a hannun miyagun mayakan ta'addancin.

Ya tabbatar wa da jama'ar da ke yankin tafkin Chadin da cewa, jami'an tsaro na hadin guiwar za su tabbatar da samuwar tsaro tare da assasa ci gaban yankin.

A wani labari na daban, dakarun sojin sama na Operation Lafiya Dole, sun samu manyan nasarori a kan mayakan ta'addanci na ISWAP da ke aika-aika a yankin tsibirin tafkin Chadi da ke Arewacin jihar Borno.

Wannan ya faru ne a ranar 24 ga watan Augustan 2020 a wani gagarumin hari da dakarun suka kai musu a karkashin Operation Hail Storm a Kira Wulgo da Sabon Tumbun.

Yankuna biyu ne na tafkin Chadi inda aka halaka manyan shugabannin ISWAP da mayakan ta'addancin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel