Yadda shugaban Amazon, Jeff Bezos ya kafa tarihi a cikin hamshakan masu arzikin duniya

Yadda shugaban Amazon, Jeff Bezos ya kafa tarihi a cikin hamshakan masu arzikin duniya

- Shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos, ya kafa babban tarihi a duniya wanda wani mahaluki bai taba kafawa a duniyar kasuwanci

- Dukiyarsa ta samu hauhawar da bata taba samu ba a ranar Laraba, inda ta kai darajar dala biliyan 204.6 duk da annobar korona da ta game duniya

- Mujallar Forbes ta bayyana cewa, hannun jari a kamfaninsa na Amazon ya yi tashin gwauron zabi inda ya kai dala 1,700 daga ranar 16 ga watan Maris

Shugaban kamfanin Amazon, Jeff Bezos, ya zama mutum na farko a fadin duniya da ya tara dukiya har ta kai dala biliyan 200.

Mujallar Forbes ta ruwaito cewa, Bezos ya mallaki dukiyar da ta kai dala biliyan 204.6 da karfe 1:50 na yammacin ranar Laraba, 26 ga watan Augustan 2020.

Hakan ta faru ne bayan da kamfaninsa na Amazon ya samu ribar kashi biyu na jimillar dukiyarsa, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Hamshakin mai kudin mai shekaru 56, wanda shine a halin yanzu yafi kowanne mahaluki kudi a duniya, ya fuskanci hauhawar arzikinsa daga dala biliyan 74 zuwa dala biliyan 204.6 a cikin shekarar 2020.

Kamar yadda lissafin mujallar Forbes ya bayyana, mamallakin kamfanin Amazon din shine mutum mafi arziki da ya taba rayuwa a duniya, duk da kuwa durkushewar kasuwanci da aka fuskanta a wannan shekarar sakamakon annobar korona.

Yadda shugaban Amazon, Jeff Bezos ya kafa tarihi a cikin hamshakan masu arzikin duniya
Yadda shugaban Amazon, Jeff Bezos ya kafa tarihi a cikin hamshakan masu arzikin duniya. Hoto daga BusinessToday
Asali: Facebook

KU KARANTA: Gwamnan Zamfara: Bakin haure ke karbar zinari suna bai wa 'yan bindiga makamai

Rahoton ya ce, kamfanin Amazon ya ci gaba da samun ci gaba a watanni kalilan da suka gabata, lamarin da ya tirsasa miliyoyin jama'a suka zauna gida amma suka ci gaba da siyan kayayyaki daga kamfanin saboda annobar korona.

Hannun jari a kamfanin ya yi tashin gwauron zabi tun daga ranar 16 ga watan Maris, yayin da aka fara siyar da shi a dala 1,700 kowanne daya.

Amazon na da darajar dala biliyan 1.72, lamarin da yasa ya zama kamfani mafi daraja na biyu a duniya bayan kamfanin Apple wanda ke da darajar dala biliyan 2.16.

Sannanen abu ne yadda annobar korona ta durkusar da kasashen duniya da kasuwanci kala-kala a fadin duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel