Dalilin da ya sa Sojojin juyin mulki suka ki sakin shugaban kasan Mali - Jonathan

Dalilin da ya sa Sojojin juyin mulki suka ki sakin shugaban kasan Mali - Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonthan, a ranar Laraba, ya gana da shugaba Muhammadu Buhari domin sanar da shi halin da aka ciki kan tattaunawar sulhu tsakanin ECOWAS da Sojojin Mali.

A cewar jawabin da mai magana da yawun Buhari, Femi Adesina, ya saki, sun zauna ne yau yayinda ake shirin taron gangamin kungiyar ECOWAS ranar Juma'a.

Jonathan ya jagoranci tawagar ECOWAS zuwa Mali ranar Asabar domin tattauna yadda za'a saki tsohon shugaban Mali, Ibrahim Keita, da kuma mayar da mulki hannun farin hula.

Jonathan ya bayyanawa Sojin Mali da suka bukaci zama kan mulki na tsawon shekaru uku cewa abu daya da ECOWAS za ta iya lamunta shine gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin farin hula ko Sojan da yayi ritaya, na tsawon watanni 6 zuwa shekara 1.

Ya kara da cewa Sojojin sun bukaci ECOWAS ta dage takunkumin da zata kakabawa kasar saboda ya fara shafan kasar.

"Mun bukaci su bari tsohon shugaba Ibrahim Keita ya koma gidansa inda za'a bashi ingantaccen tsaro, amma suka ce zai iya guduwa kasar waje, kuma ba zai dawo domin amsa wasu tambayoyinsu ba." Jonathan yace.

"Mun fada musu abinda ECOWAS zata lamunta kawai shine gwamnatin rikon kwarya, wanda farin hula ko Soja mai ritaya zai jagoranta, na tsawon watanni shida ko tara ko kuma watanni 12."

"Gwamnatin rikon kwaryan za ta shirya zabe domin mayar da mulkin Demokradiyya."

Dalilin da ya sa Sojojin juyin mulki suka ki sakin shugaban kasan Mali - Jonathan
Dalilin da ya sa Sojojin juyin mulki suka ki sakin shugaban kasan Mali - Jonathan
Source: UGC

KU KARANTA: Messi ba zai ya barin Barcelona ba sai ya biya £628m - Tsohon Dirakta a kungiyar

Jonathan ya ce shi da tawagarsa sun samu ganawa da shugaban kasan da aka kifar, wanda ya tabbatar musu da cewa yayi murabus ne don ganin damansa, kuma bai sha'awar komawa kan karagar mulki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel