Na sake kashe wata mata bayan na gudu daga hannun 'yan sanda - Cewar matashi da ya mayar da kashe mutane sana'a

Na sake kashe wata mata bayan na gudu daga hannun 'yan sanda - Cewar matashi da ya mayar da kashe mutane sana'a

Matashin nan da ake zargi da kashe mutane a jihar Ibadan, Sunday Shodipe, ya bayyana cewa ya kashe wata mata bayan ya gudu daga ofishin 'yan sanda na Mokola inda ake tsare da shi

Da yake magana a ranar Laraba 26 ga watan Agusta, a lokacin da kwamishinan 'yan sandan jihar Nwachukwu Enwonwu yake masa tambayoyi, Shodipe y bayyana cewa ya gudu daga ofishin 'yan sandan ne domin ya gabatar da wani aiki da wani boka mai suna Idris Ajani, mai shekaru 50 wanda aka kama su tare ya sanya shi.

Saurayin ya bayyana cewa bokan ya sanar da shi cewa akwai matsala babba idan har bai samu ya kubuta yaje ya cigaba da kashe mutane ba.

Na sake kashe wata mata bayan na gudu daga hannun 'yan sanda - Cewar matashi da ya mayar da kashe mutane sana'a
Na sake kashe wata mata bayan na gudu daga hannun 'yan sanda - Cewar matashi da ya mayar da kashe mutane sana'a
Asali: Facebook

Shodipe ya ce:

"Baba (Boka) ya sanar da jami'in dan sanda Funsho akan ya bude mana kofa muyi wanka, amma dan sandan yaki yadda.

'Daga baya ya sanar da jami'in cewa yana so ya sha wani ruwa a matsayin shi na boka saboda kada aljanu su shanye masa jini, duk da haka dan sandan yaki kula shi.

KU KARANTA: Bidiyo: Yadda aka tono wani yaro dan shekara 4 da rai bayan shafe kwana daya a karkashin wani gini da ya danne shi

"Bokan ya cigaba da dora mini laifi akan na sanar da 'yan sandan cewa shine yake tura ni na kashe mutane, inda yace mini da tuni an sake ni inda ban fadi gaskiya ba.

"Haka kuma ya sanar dani cewa wani abu marar kyau zai faru dashi idan har ya jima a ofishin 'yan sandan saboda dakatawa da yayi da kashe mutane sakamakon kama shi da aka yi.

"Lokacin da dan sandan ya kyaleni naje nayi wanka da misalin karfe 7 na dare, nayi amfani da wannan damar na gudu naje na kashe wata mata a Akinyele.

"Baba ne ya kara turani na kashe matar, inda ya ce na kira sunan shi, Idris Adedokun Yunusa Ajani, idan zan kashe. Na kashe matar ne domin tabbatar da lafiyar baba."

Wanda ake zargin wanda ake tsare dashi a ofishin 'yan sanda sakamakon cika da gidan yari yayi a jihar, yanzu za a kai shi wajen kamar dai yadda kwamishina 'yan sandan ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel