Muna zagaye na biyu ya mutu: Cewar Karuwar da wani mutumi ya mutu tare da ita

Muna zagaye na biyu ya mutu: Cewar Karuwar da wani mutumi ya mutu tare da ita

Wata yar gidar magajiya ta bayyana yadda wani direba wanda ya dauketa ya yanke jiki ya fadi yayinda suke zagaye na biyu cikin jima'i a gidan karuwai dake jihar Legas.

Sashen kisan kai na hukumar yan sandan jihar CIID Panti, Yaba ta kaddamar da bincike kan lamarin.

Direban motan mai suna Wuyi Jackson, wanda ke aiki da wani kamfanin mai a Ajah, ya zo tashar man Ijegun ne domin daukan man fetur, sai ya leka gidan giya ya kwankwada a unguwar Oluti.

An samu labarin cewa bayan ajiye motarsa inda ya kamata ya dauki mai, sai ya garzaya dakin otal tare da wasu abokansa misalin karfe 10 na dare.

Bayan kwankwadan kwalaben maganin karfin maza, yayi ciniki da wata karuwa mai suna Gift Ifeanyi, kuma suka shige daki.

Ashe karar kwana ne, yayinda Jackson ya shiga jima'i da Gift, kawai sai numfashinsa ya dauke kuma ya sheka barzahu daga nan.

Jaridar Vanguard ta samu labarin cewa mutumin na shirin daurin aurensa ne kuma har ya sayo buhuhunan shinkafa.

Yayinda aka bukaci jin ta bakin karuwar, Gift yace: "A daren ya zo ya sameni domin kwanciya dani, nace masa N10,000 amma ya biyani N7,000."

"Muna shiga dakin muka yi jima'i. Sai muka huta mukayi bacci. Misalin karfe 2:30 na dare ya tashe saboda mu sake komawa zagaye na biyu."

"Yayinda muke zagayen ne ya fara numfashi sama-sama kuma kafin in ankara, ya fita daga hayacinsa. Sai na daga murya domin neman agaji."

An tattaro cewa ba tare da bata lokaci ba aka garzaya da shi wani asibitin dake kusa da gidan, daga baya aka kaishi asibitin Mainland dake Yaba inda aka tabbatar da cewa ya mutu.

Kakakin hukumar yan sandan Legas, SP Bala Elkana, ya tabbatar da labarin inda yace an kammala bincike kuma ana jiran sakamako.

A yanzu dai karuwar, Gift Ifeanyi, na hannun yan sanda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel