Kotu ta dakatar da manyan motocin zuwa kudu daga aiki a jihar Kano

Kotu ta dakatar da manyan motocin zuwa kudu daga aiki a jihar Kano

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Gidan Murtala da ke birnn Kano ta dakatar da manyan motocin da ke safarar mutane zuwa kudancin Najeriya daga aiki a jihar Kano.

Alkaliyar kotun, Rakiya Lami Sani, ta zartar da hukuncin ne bayan sauraron korafin da ma'aikatar shari'a da hukumar KAROTA suka shigar a gaban kotun.

Mutawakkil Muhammad da hukumar KAROTA ne suka shigar da karar kamfanonin manyan motocin bayan sun ki bin umarnin gwamnati na komawa sabuwar tashar motoci da ke Unguwa Uku.

Da ya ke magana a kan hukuncin kotun, shugaban hukumar KAROTA, Baffa Babba Dan'agundi, ta bakin kakakin hukumar KAROTA, Nabilusi Abubakar, ya gargadi ma su manyan kotoci da su guji saba umarnin kotun.

Kotu ta dakatar da manyan motocin zuwa kudu daga aiki a jihar Kano
Kotu ta dakatar da manyan motocin zuwa kudu daga aiki a jihar Kano
Asali: UGC

Dan'agundi ya kara da cewa daga yanzu hukumar KAROTA za ta saka kafar wando daya da duk babbar motar da aka kama a cikin garin Kano.

DUBA WANNAN: Buhari ya amince da yi wa attajiran 'yan Najeriya karin kudin wutar lantarki

A cewarsa, kotun ta zartar da wannan hukunci ne saboda taurin kan da direbobin manyan motocin su ka nuna a kan umarnin da hukuma ta basu na komawa sabuwar tashar unguwa Uku.

Ya kara da cewa direbobin manyan motocin basu da lasisin izinin yin aiki a jihar Kano.

A karshe, Dan'gundi ya bukaci wadanda hukuncin ya shafa su mutunta wannan sabon hukunci domin samun lafiya da girmama dokokin jihar Kano.

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da bukatar sabon tsarin kudin wutar lantarki na NESI (Nigerian Electricity Supply Industry), kamar yadda Legit.ng Hausa ta wallafa a labarinta.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa sabon tsarin karin wutar lantarkin ba zai shafi rukunin gidajen talakawa ba.

Kazalika, shugaba Buhari ya amince da yin sassaucin biyan haraji da kaso 35% a kan sabbin mitocin wutar lantarki da za a sayo daga ketare.

A cikin watan Janairu ne hukumar kula raba hasken wutar lantarki a kasa (NERC) ta sanar da cewa za a yi karin kudin wutar lantarki a fadin kasa daga ranar 1 ga watan Afrilu.

NERC ta dakatar da kamfanonin rarraba hasken wutan lantarki (DisCos) daga shirin kara kudin wutar lantarki a cikin watan Maris saboda ballewar annobar korona.

Kazalika, a cikin watan Yuni, majalisar dattijai ta rarrashi DisCos a kan su hakura da batun kara kudin wutan lantarki har sai farkon shekarar 2021 sakamakon barkewar annobar korona a shekarar 2020.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel