Buhari ya amince da sabbin nade-nade a hukumomi 9 (Sunaye)

Buhari ya amince da sabbin nade-nade a hukumomi 9 (Sunaye)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aminta da nadin manyan shugabannin hukumomi guda tara a karkashin ma'aikatar yada labarai da al'adu.

Kamar yadda takardar amincewar ta bayyana, wacce aka mika hannun ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, ta hannun shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari, an nada Buki Ponle shugaban Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN.

Nura Sani Kangiwa ya zama Darakta Janar na hukumar karamci da yawan bude ido.

Jerin sunayen: Buhari ya amince da sabbin nade-nade a hukumomi 9
Jerin sunayen: Buhari ya amince da sabbin nade-nade a hukumomi 9. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An naɗa ɗan Najeriya Ministan Shari'a a Canada (Hotuna)

An nada Francis Ndubuisi a matsayin babban sakataren majalisar yada labarai ta Najeriya, Ebeten William Ivadaa matsayin darakta janar na hukumar, Olalekan Fadolapo a matsayin shugaban majalisar talla ta Najeriya da kuma Farfesa Sunday Enessi Ododo a matsayin babban manajan a hukumar.

Sauran sun hada da Ado Mohammed Yahuza a matsayin sakataren hukumar wayar da kai a kan al'adu, Farfesa Aba Isa Tijjani a matsayin darakta janar na hukumar gidajen tarihi na kasa da kuma Oluwabunmi Ayobami Amao a matsayin darakta janar na cibiyar wayar da kan bakaken Afrika.

Nadinsu zai fara aiki ne daga ranar daya ga watan Satumban shekarar 2020.

A wani labarin daban, Legit.ng Hausa ta kawo muku cewa an naɗa wani ɗan Najeriya mazaunin ƙasar Canada, Kelechi Madu a matsayin ministan shari'a kuma babban alƙalin yankin Alberta da ke Canada.

Madu ya wallafa rubutu a shafinsa na Twitter a kan sabon mukamin da aka naɗa shi inda ya ce dama alƙalinci tana tabbatar da yi wa kowa adalci ne kuma hakan ba zai canja ba.

Madu ya ce yana girmama dokar ƴanci ta Canada naɗa ta ce:

"Babu bambanci tsakanin mutane a dokar ƙasa, doka ta bawa kowa ƴanci iri ɗaya ba tare da tsangwama ba ko banbanci."

Ya ce zai yi amfani da wannan kalaman domin kawo cigaba ga rayuwar mutanen yankinsa na Alberta.

Ya ƙara da cewa: "Ina fatan yin aiki domin kawo sauye-sauye ta demokradiyya da dokoki tare da tabbatar da aiwatar da su cikin adalci."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel