'Yan sanda sun damke dan fashi yayin da yayi yunkurin yi wa mai takaba fyade a gaban 'ya'yanta

'Yan sanda sun damke dan fashi yayin da yayi yunkurin yi wa mai takaba fyade a gaban 'ya'yanta

- Fitaccen mai fashi da makami mai suna Tope Oladiran, ya shiga hannun jami'an 'yan sandan a jihar Legas

- An kama dan fashin ne yayin da yake hutawa a wani otal da ke birnin Ikko bayan da ya shiga gidan wata mai takaba ya yi yunkurin yi mata fyade a gaban 'ya'yanta

- Da farko ya so kwace mata waya amma ya kasa, lamarin da yasa ya jira har dare ya yi sannan ya shiga gidanta ta katanga

Wani fitaccen mai fashin na'ura mai kwakwalwa da wayoyi mai suna Tope Oladiran, ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Legas bayan fashin da yayi wa wata mata a Ori-Okuta da ke yankin Agric da ke Ikorodu wurin karfe 11 na yamma a ranar 29 ga watan Maris.

Kakakin rundunar 'yan sandan yanki na biyu, DSP Hausa Idris Adamu, ta ce wanda ake zargin ya yi yunkurin yi wa matar fyade a gaban 'ya'yanta bayan kammala musu girkin abinci.

Oladiran, wanda ya tsere bayan matar ta fasa ihu, an kama shi bayan bayanan da aka samu yana shakatawa a wani otal a jihar Legas.

Takardar ta ce: "Fashin karshe da ya kai ga aka kama Tope shine lokacin da ya je yi wa wata mata fashi a Ori-Okuta da ke yankin Ikorodu.

"Tope ya kasa kwace wayar matar amma sai ya gano cewa tana zama ne tare da yaranta biyu bayan rasuwar mijinta.

'Yan sanda sun damke dan fashi yayain da yayi yunkurin yi wa mai takaba fyade a gaban 'ya'yanta
'Yan sanda sun damke dan fashi yayain da yayi yunkurin yi wa mai takaba fyade a gaban 'ya'yanta. Hoto daga Linda Ikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda mijin mahaifiyata ya kwashe shekaru yana lalata da ni - Fatima Ada

"Wanda ake zargin ya ci gaba da zama a kusa da gidan har zuwa lokacin da dare ya rufa. Ya tsallaka katangar inda ya shiga gidan har madafinta. Ya shiga har dakin baccinta inda ya firgitata ta fara rokon shi da ya barta da ranta da na 'ya'yanta.

"Wanda ake zargin ya caje dukkan gidan inda ya samu abinci a firiji har ya dumama wa kansa. Daga nan ya nemi yi mata fyade bayan kammala cin abincin da yayi.

"Daga nan ne ta fasa ihu har jama'a suka iso don bata tallafi. Wanda ake zargin ya tsere inda ya tafi da wayar matar."

Daga bisani an kai rahoto ofishin 'yan sanda inda aka kama shi a wani otal yana shakatawa.

A halin yanzu ana ci gaba da tuhumar wanda ake zargin kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala binciken.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel