Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 12 yayin taron FEC (Hotuna)

Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 12 yayin taron FEC (Hotuna)

Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da sakatarorin dindindin guda 12 kafin a fara taron Majalisar Zartarwa ta Kasa karo na 13 da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar intanet a Abuja.

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya samu hallartar rantsarwar da aka yi a dakin taron majalisar da ke gidan gwamnati.

Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 12 yayin taron FEC (Hotuna)
Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 12 yayin taron FEC (Hotuna)
Asali: Twitter

Sakatarorin da aka nada tun a watan Yuni cikin wata sanarwa da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi Esan ta fitar suna hada da : Belgore Shuaib Mohammad Lomido, Kwara; Akinlade Oluwatoyin, Kogi; Ekpa Anthonia Akpabio, Cross River; Alkali Bashir Nura, Kano; Ardo Babayo Kumo, Gombe da Anyanwutaku Adaora lfeoma, Anambra.

Saura su ne Udoh Moniloja Omokunmi, Oyo; Hussaini Babangida, Jigawa; Mohammed Aliyu Ganda, Sokoto; Mahmuda Mamman, Yobe; Meribole Emmanuel Chukwuemeka, Abia daTarfa Yerima Peter, Adamawa.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona

Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 12 yayin taron FEC (Hotuna)
Buhari ya rantsar da manyan sakatarori 12 yayin taron FEC (Hotuna)
Asali: Twitter

Shugaban kasar ya kuma rantsar da kwamishinonin hukumar kula da maaikatan gwamnatin tarayya, Idahagbon Henry, da na hukumar tattara haraji da rabar da ita, Usman Hassan.

Ministocin da suka hallarci taron a zahiri sune: Godswill Akpabio, Niger Delta; Abubakar Malami, Ministan sharia; Alhaji Lai Mohammed, ministan labarai; Hajiya Zainab Ahmed, ministan kudi da tsare tsaran kasa; Mohammed Bello, minsitan Abuja, Sulieman Adamu, ministan albarkatun ruwa.

Saura da suka hallarci taron sune (SGF), Boss Mustapha; shugaban maaikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mashawarcin shugaban kasa kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (murabus).

Shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Yemi Esan da sauran ministocin sun hallarci taron ne ta hanyar intanet daga ofisoshinsu.

Ku saurari karin bayani ...

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel