Tsadar farashi: Shinkafa ta fara gagaran mutane a jihar Kano ci - Bincike

Tsadar farashi: Shinkafa ta fara gagaran mutane a jihar Kano ci - Bincike

Mazauna jihar Kano sun magantu kan yadda farashin shinkafa yayi tashin gwauron zabo duk da yawan masu noman shinkafa a jihar, rahoton Daily trust.

Kamar yadda akayi ittifaki, shinkafa ce abinci mafi farin jini a Najeriya, amma ta fara gagaran talaka yanzu bisa tsadarta kuma an fara kokawa.

Manoma da yan kasuwan shinkafa kuwa sun bayyana cewa duk da yawan kamfanonin sarrafa shinkafa ta jihar, abincin tayi tsada ne sakamakon a tashin gwauron zabon da shinkafa da ake fitarwa daga gonaki kafin cire bawon tayi da kuma shisshigin dillalai.

Binciken Chronicle cikin kasuwa ya nuna cewa farashin buhun shinkafar gida yanzu ya zama N22,000 zuwa N24,000 sabanin N16,000 da ake sayarwa a Junairun 2020.

Hakazalika an samu cewa ana sayar da shinkafa da ake fitarwa daga gonaki kafin barewa N16,000 sabanin N9,500 da aka sayar a Junairun 2020.

Tsadar farashi: Shinkafa ta fara gagaran mutane a jihar Kano ci - Bincike
Tsadar farashi: Shinkafa ta fara gagaran mutane a jihar Kano ci - Bincike
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Matsina tattalin arziki: Yan Najeriya da dama zasu fada talauci nan da yan watanni - Masana

Wani mazaunin Hotoro quaters, Isa Shehu, ya bayyanawa Chronicle cewa "Mun yi tunanin rufe iyakokin Najeriya da hana shigo da shinkafar gwamnati da tallafin da gwamnatin tarayya ta baiwa manoman shikafa, zai saukakewa talakawa farashin."

"Amma yanzu muna gani cewa ba'a cimma manufar da akayi niyya da kulle iyakokin ba saboda shinkafa ta zama tamkar zinari ga talaka yanzu.

Hakazalika, wani karamin mai kamfanin sarrafa shinkafa, Musa Idris, ya ce tashin gwauron zabon shinkafa daga gonaki ya tilastawa masu sarrafa shinkafa kara farashi ko kumasu kulle masana'antunsu saboda ba zai yiwu ba."

Wani dan kasuwa mai sayan shinkafan dake fitowa daga gonaki, Bala Sani Maitan, ya ce yawancin abokan aikinsa yan kasuwa ne kawai masu sayan danyen shinkafa suna boyewa daga baya su sayar da tsada.

Yayinda aka tuntubi kwamishanan kasuwanci da masana'antun jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mukhtar, ya ce gwamnati na sane da abinda ke faruwa kuma zata gana da masu ruwa da tsaki domin ganin inda matsalar take da yadda za'a maganceta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel