Fani-Kayode ya nemi afuwar dan jaridar da ya fada wa kalaman wulakanci

Fani-Kayode ya nemi afuwar dan jaridar da ya fada wa kalaman wulakanci

Femi Fani-Kayode, lauya kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama, ya nemi afuwar Eyo Charles, dan jaridan Daily Trust da ya zaga a wurin taron manema labarai a Calabar.

Fani-Kayode a ranar Talata ya ce ba zai bayar da hakuri ba ko neman afuwa game da bidiyon sa yana zagin dan jarida da ya bazu a kafafen watsa labarai da dandalin sada zumunta.

Charles ya tambaye shi ne idan akwai wani da ke daukan nauyin tafiye tafiyen da ya ke yi zuwa wasu jihohin Peoples Democratic Party (PDP), daga nan sai ya fara zage zage da daga murya.

Fani-Kayode ya nemi afuwar dan jaridar da ya zazzaga
Fani-Kayode ya nemi afuwar dan jaridar da ya zazzaga
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Messi ya ce zai bar Barcelona

A sanarwar da ya fitar a ranar Laraba a shafinsa na Twitter, Fani-Kayode ya ce, "Bayan gana wa da mashawarta na, ina son in bayyana cewa na janye kalmar wawa da na yi amfani da ita yayin abinda ya faru tsakani na da dan jarida a Calabar.

"Ina da abokai da dama yan jarida kuma na bata musu rai a lokacin da na fusata na yi amfani da irin wannan kalmomin. Na yi nadamar yin hakan."

Ya kuma musanta zargin da aka yi na cewa ya yi barazanar dukkan dan jaridar inda ya bukaci duk wani mai hujjar nuna hakan ya bayyana wa duniya.

"Ba zan taba tunanin dukkan dan jarida ba. Shekaru 30 da suka shude, na yi aiki da yan jarida tare da kare su, na kuma yi yaki don tabbatar da cewa kowa na da ikon bayyana raayinsa," in ji tsohon ministan.

Ya cigaba kara da cewa, "ba zan kasance cikin wadanda za su ci mutuncin masu wannan sanaar mai mutunci ba. Ina fata wannan zai sassauta zuciyar wadanda abinda ya faru ya bata wa rai. Ba zan sake waiwayar lamarin ba."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel