Matsin tattalin arziki: Yan Najeriya da dama zasu fada talauci nan da yan watanni - Masana

Matsin tattalin arziki: Yan Najeriya da dama zasu fada talauci nan da yan watanni - Masana

Dirakta Manaja na kamfanin Financial Derivatives, Bismarck Rewane, ya ce tattalin arzikin Najeriya zai durkushe nan da watanni masu zuwa a rubi'in kusa da karshen shekarar 2020.

Rewane ya bayyana hakan ga wakilan The Punch a ranar Talata inda yayi tsokaci kan Alkaluman da hukumar lissafin Najeriya NBS ta saki kan yanayin tattalin arzikin Najeriya.

Yace: "Tattalin arzikin Najeriya zai shiga durkushewa a rubi'in kusa da karshen shekarar 2020 kuma akwai yiwuwan ganin karkataccen farfadowa yayinda mutane kan iya sake kamuwa da cutar COVID19 wanda ka iya sabbaba sake kakaba dokar kulle."

"Asusun Lamunin Duniya IMF ta yi hasashen cewa tattalin arzikin Najeriya zai durkushe da maki -5.4% a shekarar 2020."

"Abin farin ciki kawai shine sassauta dokar kulle da kuma tashin da farashin danyen mai ke yi a kasuwar duniya na iya saukaka durkushewar tattalin arzikin nan da karshen shekara."

Rewane ya ce durkushewar tattalin arzikin Najeriya na nufin cewa za'a samu karuwan rashin aiki yi.

Bayan haka, ya kara da cewa za'a ga yawan mutanen da zasu fada bakin talauci saboda karancin kudin da rashin aikin yi.

Kan illan da durkushewar zai yiwa yan kasuwa, yace "Yan kasuwa masu sanya hannun jari sun san tattalin arzikin kasar na iya durkushewa saboda rahoton PMI ya nuna yadda abubuwa ke gudana."

Matsina tattalin arziki: Yan Najeriya da dama zasu fada talauci nan da yan watanni - Masana
Rewane
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa tattalin arzikin kasar Najeriya ya durkushe a cikin shekarar nan ta 2020. Alkaluman da aka fitar na rubu’in bana sun nuna tattalin kasar bai iya motsawa gaba ba.

Asali ma tattalin kasar ya durkushe ne da maki – 6.10%, hakan ya na nufin tattalin arzikin Najeriya ya motsa baya ne maimakon ya yi gaba a tsakiyar wannan shekara.

Jaridar Daily Trust ta ce wannan ne mafi munin halin da aka shiga tun shekarar 2010. Tsakanin 2016 da 2017 tattalin kasar ya karye, amma munin bai kai irin haka ba.

Bloomberg ta yi hasashen tattalin arzikin kasar nan zai karye da 4%, a karshe alkaluman NBS sun nuna cewa tasirin COVID-19 ya jawo tattalin ya durkushe da kashi 6%.

Hakan ya na zuwa ne jim kadan bayan an samu rahoton cewa mutane fiye da miliyan 21 ba su da aikin yi a Najeriya. Wannan zai iya haddasa yawan aukuwar laifuffuka.

Babban abin da ya jawowa Najeriya wannan durkushewar tattali ita ce annobar COVID-19, wanda ta nakasa kasashen Duniya da-dama, daga ciki har da Amurka da Ingila.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel