Yadda mijin mahaifiyata ya kwashe shekaru yana lalata da ni - Fatima Ada

Yadda mijin mahaifiyata ya kwashe shekaru yana lalata da ni - Fatima Ada

Fatima Ada Isiaku mace ce da ta fuskanci cin zarafi yayin da take da shekaru biyar kacal a duniya. Ta bayyana labarinta mai cike da al'ajabi a ranar Talata.

Kamar yadda Ada ta sanar, mijin mahaifiyarta, wanda take kallo a matsayin mahifinta, shine ya fara saka yatsansa a gabanta, lamarin da ya dagula mata lissafi.

"A lokacin da na cika shekaru bakwai kuwa, lamarin ya yi kamari. Na zama tamkar baiwarsa don yana kwanciya da ni a gidan da mahaifiyata take duk da bata da wannan sanin," ta ce a yayin da take jawabi a wani taro da aka yi na majalisar dinkin duniya a kan cin zarafin jinsi a Najeriya.

Duk wani kokarinta na samun taimako ya gagara, saboda wacce za ta sanarwa lamarin ba za ta yadda da hakan na faruwa ba.

Ta jure mummunan cin zarafin na tsawon shekaru, duk a shirmenta mai lalata da ita ne mahaifinta, Channels Tv ta ruwaito.

"A gaskiya da farko tsammanina shine mahaifina, ban taba sanin ba shi bane. A lokacin da nake da shekaru 14 a duniya ne mahaifiyata ta gano abinda ke faruwa kuma ta tabbatar da cewa ba shine mahaifina ba," tace.

Bayan shekarun da ta kwashe tana kokarin fahimtar da mahaifiyarta, sai ta fuskanci wani tozarcin kafin gaskiya tayi halinta. Mahaifiyarta da kanta ta duba budurcinta inda ta gane babu shi.

Yadda mijin mahaifiyata ya kwashe shekaru yana lalata da ni - Fatima Ada
Yadda mijin mahaifiyata ya kwashe shekaru yana lalata da ni - Fatima Ada. Hoto daga Daily Trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Bayan karbar albashi, ya tafi shakatawa da karuwarsa inda ta tsinke masa mazakuta sakamakon rikici

Bayan dawowarta gida daga makaranta a cikin barikin sojojin da suke, mahaifiyarta ta karbeta ba yadda ta saba ba.

"A lokacin da na dawo daga makaranta, kannaina sun gaisheta hakazalika nima, amma sai ta amsa musu, ni kuwa bata amsa gaisuwata ba.

"Ta bukaci in tsaya a waje yayin da ta sanar da kannaina cewa su shiga ciki kuma kada su kuskura su fito.

"A nan ta saka na cire dan kamfai na inda ta watsa ruwa a gabana kuma ta ga ya shige. A take ta fasa ihu tana cewa 'dama ke ba budurwa bace?'" Tace

A wannan lokacin shekarunta 14 kacal, Fatima bata san komai game da irin wannan kalaman ba kuma bata san me ake nufi da budurwa ba.

"Na bata amsa da, 'wacece budurwa?'. A take ta ganar da ni cewa dama namiji ya saba kwanciya da ni. Babu shakka ko wani alhini nace mata mahaifina ne," ta bayyana a taron.

Fatima ta dauka tsawon lokaci tana yi wa mahaifiyarta bayani kafin ta amince da kalamanta.

Kamar yadda tace, ba lalata kadai mijin mahaifiyarta yake yi da ita ba, ya yi nasarar cusa tsanarta a zuciyar mahaifinta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel