Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ya kaure a birnin Barcelona kan shirin da Messi yake na tafiya

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ya kaure a birnin Barcelona kan shirin da Messi yake na tafiya

Dubunnan mazauna birnin Cataloniya a kasar Espana suna gudanar da zanga-zanga kan matsalar da dan kwallon kungiyar kwallon Barcelona, Lionel Messi, ya samu da shugabannin kungiyar.

Shahrarren dan kwallon ya bayyanawa shugabannin kungiyar kwallon cewa zai bar Barcelona nan take bayan sama da shekaru 20 yana taka musu leda.

Dan kasar Argentinan na shirin hannun riga da kungiyar kwallon da ya kasance yana bugawa wasa tun yana dan yaro saboda rashin jituwa da shugabancin kungiyar karkashin jagorancin Josep Bartomeu.

Mutanen sun yi tururuwa a kusa filin kwallon kungiyar da ofisoshin shugabanin domin zanga-zanga.

Wasu daga cikin masu zanga-zangan na iwun 'Bartomeu yayi murabus'

Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ya kaure a birnin Barcelona kan shirin da Messi yake na tafiya
Yanzu-yanzu: Zanga-zanga ya kaure a birnin Barcelona kan shirin da Messi yake na tafiya
Asali: UGC

Bayan kimanin shekaru 20, Lionel Messi ya shaida wa ƙungiyar Barcelona cewa yana son barin kungiyar.

Kungiyar ta tabbatar a ranar Talata cewa ɗan wasan ɗan asalin ƙasar Argentina ya rubuta mata wasika cewa yana son ya tafi.

Sanarwar na zuwa ne kimanin kwanaki 11 bayan kayan da ƙungiyar ta sha na 8 - 2 a hannun Bayern Munich, daya daga cikin kaye mafi muni a tarihin kwallon ƙafa.

Wannan shan kayen ya ƙara wa kungiyar abin takaici - duba da cewa tun 2007-08 ba su ci kofi ba ga shan kaye kamar yadda Sky reports ta ruwaito.

Messi ya lashe Ballon d'Or guda shida yayin zamansa a Barcelona a matsayin ɗan wasan daga cikin mafi girma a duniya.

Ya kuma taimaka wa kungiyar ta lashe kofin gasar wasar ƙwallon ƙafa na Spain guda 10 da gasar ƙwallon wasan 'Champions League' hudu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel