Dakarun Sojin Najeriya sun damke yan bindiga 150 a Zamfara, sun kashe 1

Dakarun Sojin Najeriya sun damke yan bindiga 150 a Zamfara, sun kashe 1

Dakarun Sojin Najeriya karkashin atisayen Operation Sahel Sanity, sun damke yan bindiga akalla 150 kuma sun hallaka daya a jihar Zamfara.

Mukaddashin diraktan harkokin yada labarai rundunar, Birgediya Janar Benard Onyeuko, ya bayyana hakan a Faskari, jihar Katsina ranar Talata.

Onyeuko ya ce Sojin sun gano wata mabuyar yan bindigan dake Gadan Zaima inda sukayi ram da su.

Ya kara da cewa yan bindigan da aka damke suna hannun yan sanda kuma an kaddamar da bincike kansu.

Ya ce za'a mikasu hannun yan sanda na ba da dadewa ba.

Yace: "A ranar 23 ga Agusta, 2020, rundunar Soji sun aiwatar da binciken leken asiri kuma suka kai hari wani wajen hakar ma'adinai dake hanyar Gadan Zaima-Zuru a karamar hukumar Bukuyyum na jihar Zamfara inda yan bindiga ke boyewa."

"Yayin harin, dakarun sun damke mutane 150 kuma sun kwace bindigogin gargajiya 20. An kashe daya daga cikinsu yayinda yake kokarin guduwa."

Onyeuko ya kara da cewa gabanin harin Lahadi, an damke yan bindiga da dama kuma an kashe uku a ranar 20 da 21 ga Agusta a wasu wurare a jihar.

KU KARANTA: Na cika alkawarina na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya - Buhari

Dakarun Sojin Najeriya sun damke yan bindiga 150 a Zamfara, sun kashe 1
Dakarun Sojin Najeriya sun damke yan bindiga 150 a Zamfara, sun kashe 1
Asali: Twitter

A bangare guda, Dakarun sojin sama na Operation Lafiya Dole, sun samu manyan nasarori a kan mayakan ta'addanci na ISWAP da ke aika-aika a yankin tsibirin tafkin Chadi da ke Arewacin jihar Borno.

Wannan ya faru ne a ranar 24 ga watan Augustan 2020 a wani gagarumin hari da dakarun suka kai musu a karkashin Operation Hail Storm a Kira Wulgo da Sabon Tumbun.

Yankuna biyu ne na tafkin Chadi inda aka halaka manyan shugabannin ISWAP da mayakan ta'addancin.

Dakarun sun kai samamen ne bayan gamsassun rahotanni da suka samu da ke bayyana cewa shugabanne ISWAP da mayakan su sun koma Sabon Tumbun saboda ragargaza su da aka yi a yayin da suke tsibirin kusa da Tumbuma Baba.

Hakazalika, manyan kwamandojin ISWAP a kalla 15 aka halaka a Kira Wulgo, inda suka mayar babbar hedkwatarsu kuma wurin horarwa mayakan ta'addancin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel