Na cika alkawarina na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya - Buhari

Na cika alkawarina na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya cika alkawarinshi na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya.

A ranar Talata, hukumar kiwon lafiyan duniya WHO ta alanta cewa Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afrika sun barranta daga cutar shan inna.

Yayin magana a taron da ya gudana ta yanar gizo, Buhari ya ce ya yiwa yan Najeriya alkawarin cewa ba zai sauka daga mulki ba sai ya kawar da cutar, kuma yanzu ya cika alkawarinsa.

"Wannan taro ne mai tarihi. Ina iya tunawa bayan hawa mulki a 2015 na ce ba zan mika ragamar mulki ga magaji na ba da sauran cutar shan inna a Najeriya," Buhari yace

"Wannan tabbaci cika alkawari na ne, ba ga yan Najeriya kadai ba, amma ga yan nahiyar Afrika."

Buhari ya taya nahiyar Afrika murna da shugabancin gamayyar kasashen afrika bisa wannan nasara.

KU KARANTA: Da na shiga matsala, Nasir El-Rufai ne ya fara taimakona inji Muhammadu Sanusi II

Na cika alkawarina na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya - Buhari
Na cika alkawarina na kawo karshen cutar shan inna a Najeriya - Buhari
Asali: UGC

Mun kawo muku rahoton cewa hukumar tabbatar da karewar cutar shan inna a nahiyar Afrika ARCC ta alanta cewa Najeriya da sauran kasashen Afrika sun barranta daga cutar shan inna a ranar Talata.

A cewar hukumar lafiyan duniya WHO, wannan ya kawo karshen muguwar cuta na biyu a nahiyar Afrika bayan cutar karambau shekaru 40 da suka gabata.

ARCC ta sanar da hakan ne bayan shekaru da yawa suna bibiyan lamarin shan inna, suna bayar da rigakafi.

A 1996, shugabannin kasashen Afirka sun lashi takobin kawo karshen shan inna a taron kungiyar hada kan kasashen Afirka OAU da ya gudana a Yaounde, kasar Kamaru.

A lokacin, cutar shan inna na nakasa yara 75,000 kowani shekara a nahiyar.

Shekarar 2016 ne karshe da aka samu mai cutar shan inna a Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel