Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya

Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya

Femi Fani Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama ya rufe wani ɗan jarida, Eyo Charles da zagi saboda ya masa tambaya a yayin taron manema labarai a Calabar jihar Cross Rivers a makon da ya gabata.

Tsohon ministan wadda ya fara ziyarar jihohin da Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ke mulki tun a watan Yuli ya ziyarci Cross Rivers a makon da ya gabata.

The Cable ta ruwaito cewa a karshen ziyarar, ya kira taron manema labarai inda ya yaba wa ayyukan da Gwamna Ben Ayade na jihar Cross Rivers ya yi.

Baya ga yabon, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tallafawa jihar duba da ƙarancin kuɗi da ta ke da shi.

Eyo, wani ɗan jarida mai yi wa Daily Trust aiki ya tambayi tsohon ministan ko wani ne ya dauki ɗawainiyar tafiye-tafiyen da ya yi hakan yasan Fani-Kayode ya fusata ya fara zage-zage.

Fani-Kayode ya kira ɗan jaridar 'wawa' kuma ya ce shi ba talaka bane da zai nemi wani ya biya masa kuɗin tafiye-tafiyen sa.

Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya
Yadda tsohon minista ya 'zazzagi' dan jarida saboda ya masa wata tambaya
Asali: Twitter

Ga wani sashi cikin abinda tsohon ministan ya faɗi.

"Bari in faɗa a talabijin kowa ya gani. Wane irin tambayar banza ne wannan? Daukan nauyin wa? Ka ko san da wanda ka ke magana? Ba zan amsa tambayar wannan mutumin ba.

"Wace irin tambayar cin mutunci ne wannan? Wace irin ɗaukan nauyi? Wane zai iya bani kuɗi? Da wa kake tunanin ka ke magana? Ka je ka yi ƙaran kan ka zuwa shugaban ka, kada ka zage ni a nan, ba zan amsa tambayar wannan mutumin ba.

"Na gani a fuskarka tun kafin ka iso nan cewa kai wawa ne. Kada ka sake min irin wannan maganar. Ko ka san da wanda ka ke magana? Ƙaramin tunani ka ke da shi, kada ka ɗauka kowa irin ka ne.

DUBA WANNAN: Hotuna: Matawalle ya gabatarwa Buhari gwala-gwalai da wasu ma'adinai da aka hako a Zamfara

"Tun shekarar 1990 na ke siyasa ... An sha daure ni, na wahala. An yi min bita da ƙulli fiye da sauran ƴan siyasar da ka ke bi domin su baka na kashe wa. Kada ka sake min irin wannan, ni ba talaka bane kuma ba zan taba ƴin talauci ba."

Fani-Kayode ya cigaba da kumfar baki da zage-zage inda ya tunatar da ɗan jaridar cewa ya rike muƙamin minista a baya kuma shi lauya ne saboda haka cin fuska ce wani ya yi tsammanin yana bukatar a biya masa kuɗin tafiye-tafiyen sa.

Bayan ya kammala zazzage abinda ke cikinsa, ya tambayi ko sauran ƴan jaridar na da sauran tambaya inda suka ce a'a sannan ya yi tafiyarsa.

Babban sakataren watsa labaran gwamna Ayade, Christian Ita ya yi ƙoƙarin bawa Ministan haƙuri amma bai haƙura ba ya cigaba da zagin ɗan jaridar.

A watan Yuli, Masarautar Zamfara ta naɗa Fani-Kayode sarautar "Sadaukin Shinkafa" wadda hakan ya janyo wasu masu sarauta suka yi murabus.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel