Hotuna: Matawalle ya gabatarwa Buhari gwala-gwalai da wasu ma'adinai da aka hako a Zamfara

Hotuna: Matawalle ya gabatarwa Buhari gwala-gwalai da wasu ma'adinai da aka hako a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle a ranar Litinin 24 ga watan Agusta ya kai wa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Matawalle ya gabatarwa da shugaban kasar gwala-gwalan da wasu ma’adinai daban-daban da aka hako a jihar Zamfara.

Alhaji Bashir Hadejia ne ya yi wa Gwamna Matawalle rakiya yayin ziyarar da ya kai fadar shugaban kasar a daren jiya Litinin domin gabatar wa shugaba Buhari ma'adinan.

Hotuna: Matawalle ya gabatarwa Buhari gwala-gwalai da wasu ma'adinai da aka hako a Zamfara
Hotuna: Matawalle ya gabatarwa Buhari gwala-gwalai da wasu ma'adinai da aka hako a Zamfara
Asali: Twitter

Hadimin shugaban kasa a kan kafafen watsa labarai, Buhari Sallau yana daga cikin wadanda suka wallafa hotunan ziyarar a dandalin sada zumunta.

Ya rubuta cewa,

Shugaba Muhammadu Buhari a daren jiya a gidansa, wato gidan gwamnati da ke Abuja ya karbi bakuncin Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Muhammad Matawalle da Alhaji Bashir Hadejia ya yi wa rakiya.

Gwamna Matawalle ya ziyarci gidan gwamnatin ne domin ya gabatar da gwala-gwalai da wasu maadinai masu daraja da aka hako a jiharsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164