An gurfanar da basarake a kotu kan zargin yin rantsuwa a kan karya

An gurfanar da basarake a kotu kan zargin yin rantsuwa a kan karya

- An maka basarake a gaban kotu saboda yin karya a yayin da ya tafi rantsuwa a kotu

- An zargin zaɓaɓɓen sarkin garin Agwu, Cif Emmanuel Muodebel Ogbonna ne da ƙaryar cewa shi Injiniya ne

- Wanda ake zargin ya musanta zargin inda kuma ya nemi a bayar da shi beli saboda matsayarsa na mai sarauta

Rundunar Yan sandan Jihar Enugu a ranar Litinin ta gurfanar da wani zababben mai sauratar gargajiya a garin Ogugu da ke karamar hukumar Agwu na jihar, Cif Emmanuel Ogbonna a gaban kotu saboda karya.

Ƴan sandan na zargin Ogbonna da yin rantsuwa alhalin ƙarya ya ke yi na cewa shi injiniya ne amma ba shi da takardun shaidan cewa shi injiniya ne.

An gurfanar da basarake a kotu kan zargin yin rantsuwa a kan karya
An gurfanar da basarake a kotu kan zargin yin rantsuwa a kan karya
Asali: Twitter

Tuhumar biyu da aka masa sun ce, "Kai Cif Emmanuel Muodebel Ogbonna a shekarar 2011 a babban kotun Enugu na yankin Agwu ka yi rantsuwa cikin wata takarda mai lamba HAW/01/2011 tsakanin Cif Emmanuel Muodebel Ogbonna da Jonas Uchenwa da wasu mutum shida ka yi rantsuwa cewa kai injiniya ne alhalin ka san cewa ba ka da takardar shaidan hakan, hakan laifi ne da ya saba da sashi na 145 da 146 na Criminal Code, Cap 30, Vol II Na jihar Enugu Nigeria, 2004.

"Kuma kai Cif Emmanuel Muodebel Ogbonna a kotun da aka ambata a baya ka gabatar da kanka a matsayin ƙwararen injiniya kuma ka san hakan ba gaskiya bane saboda haka ka aikata laifi da ya saba wa sashi na 460 na Criminal Code, Cap 30, Vol II na jihar Enugu Najeriya 2004."

Wanda ake yi wa zargin ya musanta aikata laifukan.

Lauyansa, Nwabueze Ugwu ya nemi a bayar da belinsa inda ya ce, "wanda ake zargin tsoho ne kuma zaɓaɓɓen basarken garin garinsa. Matsayinsa abin duba wa ne; wanda ake zargin shugaban al'umma ne; a kullum yana fadarsa kuma bai kamata ya bar fadarsa ba. Muna rokon a amince da bukatar mu saboda wannan dalilin na saninsa da aka yi."

Ɗan sanda mai shigar da ƙarar ya ce ba zai hana a bayar da belin ba muddin wanda ake zargin zai gabatar da wadanda za su tsaya masa tare da adireshi sahihi.

Yayin yanke hukunci a kan belin, shugaban kotun, Nwebiem ya bayar da belin basaraken a kan kudi N300,000 kuma ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Satumba domin zartar da hukunci na karshe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel