Yadda na zama direban jirgin sama daga aikin tura baro - Dan Najeriya ya bada labari mai ban sha'awa
- Wani dan Najeriya da rayuwa tayi masa kyau mai suna Wilfred Asuquo, ya bayyana cewa ilimi yana daya daga cikin hanyar dacewa a rayuwa
- Wilfred ya ce neman ilimi da ya fita yi shi ya canja masa rayuwa, inda ya tashi daga aikin turin baro a shekarar 1997 zuwa direban jirgin sama a shekarar 2009
- Dan Najeriya ya ce yana da matukar muhimmanci mutum ya nemi ilimi saboda hatta mutanen da suke da kudi da basu da ilimi suna nemo masu ilimi su jawo su a jikinsu
Wani saurayi dan Najeriya mai suna Wilfred Asuquo, yayi amfani da kanshi a matsayin misali kan yadda ilimi yake da matukar muhimmanci wajen samun nasara a rayuwa.
A shafinsa na LinkedIn, mutumin ya shawarci mutanen da suke ganin cewa neman ilimi bashi da muhimmanci wajen samun nasarar rayuwa, inda ya kara da cewa hatta manyan masu kudi da basu yi karatu ba suna nemo masu ilimi ne su ja su a jiki wajen taimaka musu suyi kasuwancinsu.

Asali: Facebook
Yace ya ga muhimmancin ilimi bayan ya bar kauyensu a lokacin da yake da shekaru 16. Inda ya wallafa tsohon hotonsa, ya ce a shekarar 1997 bashi da ilimi turin baro yake yi ya samu kudi.
KU KARANTA: Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa
A hoton za a ganshi rike da baro din. Ya kara da cewa yana kammala karatunsa na difloma sai komai ya canja a rayuwarsa ya zama direban jirgin sama.
Wilfred ya ce ilimi tare da kuma darasi da ya dauka a makarantar sakandare su suka taimaka masa ya samu dacewa a rayuwa.
Dan Najeriyan ya ce kamar yadda ilimi yake da matukar muhimmanci, yana kuma da muhimmanci mutum ya koyi yadda ake zama da jama'a.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng