Saboda carar zakaransa da sassafe: Kotu ta ci wani tsoho tarar N77,304

Saboda carar zakaransa da sassafe: Kotu ta ci wani tsoho tarar N77,304

- Jami'an tsaro da ke birnin Castiraga Vidardo da ke Lombardy a kasar Italiya, sun ci tarar wani tsoho har N77,304 a kan zakaransa

- An kama zakaran tsohon mai shekaru 83 mai suna Carlino da laifin fara cara wurin karfe 4:30 na safe inda yake kaiwa har karfe 6:00 na safe

- Jami'an tsaron su samu korafe-korafen mazauna yankin, kuma sun bibiyi lamurran zakara Carlino har suka tabbatar da laifin

Wata hukuma ta bukaci wani tsoho mai shekaru 83 a duniya da ya biya tarar N77,304 bayan ya kasa hana zakaransa cara da karfe 4:30 na asubahi, wanda wasu daga cikin makwabtansa suka koka da hakan.

Angelo Boletti, tsohon ma'aikacin gwamnati ne wanda yayi murabus a kasar Italiya. Dan asalin garin Castiraga Vidardo ne da ke Lombardy kuma an kama shi da laifin take dokar kasar.

Dokar kasar ta bada umarnin ajiye dabbobin da ake kiwo da nisan a kalla mita goma daga gidajen makwabta.

Amma babban abinda yasa aka kai kara tsoho Angelo Boletti, shine yadda zakaransa mai suna Carlino yake cara da asubahi wurin karfe 4:30 na safe kuma yana tashin makwabta daga bacci.

Saboda carar zakaransa da sassafe: Kotu ta ci wani tsoho tarar N77,304
Saboda carar zakaransa da sassafe: Kotu ta ci wani tsoho tarar N77,304. Hoto daga Daily Trust
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sokoto: Yadda 'yan bindiga suka sace amarya da mai jego

Bayan jami'an 'yan sandan yankin sun samu korafe-korafe a kan yadda zakaran ke tada jama'a baccin safe, sun fara kiyayewa tare da lura da Carlino.

Bayan tabbatar da zarginsu na carar sassafe, an yanke hukuncin cin tarar tsohon N77,304.

"Ban san me zan ce ba. Wacce bukata ce kuma garesu a yanzu?" Boletti ya sanar da wata mujallar kasar Italiya.

"Da tun farko sun sanar da ni a kan nisanta zakaran daga garesu. Ban gane bane."

Emma Perfetti, shugaban Castiraga Vidardo, ya sanar da manema labarai cewa jami'an yankin basu da wata mafita da ta wuce su dauka mataki, saboda tsananin korafe-korafen da suka samu daga mazauna yankin.

Jami'an 'yan sandan sun labe a wurin gidan Boletti da dare, kuma sun tabbatar da cewa Carlino ya fara cararsa wurin karfe 4:30 na safe sannan ya ci gaba har wurin karfe 6:00 na safen.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel