Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 3 da ke shirin rubuta jarabawa

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 3 da ke shirin rubuta jarabawa

Wasu miyagu da ake zargin 'yan bindiga ne sun shiga gidajen mazauna yankin Damba-Kasaya da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

An gano cewa, 'yan bindigar sun iza keyar yara uku 'yan makaranta da ke bita a kan jarabawar kammala aji uku na sakandare da za su fara.

Bawa Wakili, wani mazaunin yankin ya zanta da jaridar The Cable inda yace 'yan bindigar sun zo "da yawansu kamar yadda suka saba", kuma sun dinga harbi har suka kammala abinda suka yi niyya.

Ya ce: "Sun yi garkuwa da jama'a da yawa a kauyen. Daga nan sun shiga wata makarantar kudi inda suka kwashe dalibai masu shirin rubuta jarabawar kammala aji uku ta sakandare.

"Ba zan iya cewa mutum nawa suka yi garkuwa da su ba amma sun tafi da mutane da yawa.

"Sojojin da suka zo kawo agaji sun juya inda suka bar wasu daga cikin mazauna kauyen a kan hanyar da suka bi su don raka su ceto wadanda aka sacen.

“Mazauna kauyen sun ci gaba da bibiyar masu garkuwa da mutanen duk da barinsu da sojojin suka yi. Ganin hakan ne yasa 'yan bindigar suka fara harbinsu har suka kashe mutum daya."

Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 3 da ke shirin rubuta jarabawa
Kaduna: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dalibai 3 da ke shirin rubuta jarabawa. Hoto daga HumAngle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kisan matar babban limami a Arewa: 'Yan sanda sun kama mutum 3 da ake zargi

A wani labari na daban, wasu jama'a da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da sabuwar amarya tare da wata mai jego a kauyen Sutti da ke karamar hukumar Tangaza ta jihar Sokoto.

Wata majiya ta ce, an sace amaryar ne yayin da jerin tawagar motoci ke kai ta gidan mijinta a ranar Laraba, 19 ga watan Augusta.

Kamar yadda majiyar ta ce, mai jegon ita ce matar Magajin Garin Sutti kuma har gida aka bi ta aka saceta da jinjirinta a daren Alhamis.

Majiyar ta sanar da Daily Trust cewa, har yanzu ba a san yawan jama'ar da 'yan bindigar suka sace ba a kan babbar hanyar Balle zuwa Tangaza a ranar Laraba.

"'Yan kasuwar na dawowa daga Tangaza inda suka nufa Balle a motocin haya biyu. Sun fada kan shingen kan titi wanda 'yan bindigar suka saka, a take kuma suka umarcesu da su fito daga cikin ababen hawan sannan suka yi awon gaba da su.

"Har zuwa ranar Juma'a da ta gabata, ba a ji komai game da su ba kuma ababen hawansu na nan wurin inda aka iza keyarsu," majiyar ta kara da cewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel