Dalibin Najeriya da yake amfani da sana'ar siyar da Koko yake biya kanshi kudin karatu a jami'a

Dalibin Najeriya da yake amfani da sana'ar siyar da Koko yake biya kanshi kudin karatu a jami'a

- Dalibin aji daya a jami'a, Jimoh John Yakubu, ya ce yana samun kudi ya kuma biya kudin makarantar shi ne ta hanyar siyar da koko

- Dalibin mai shekara 21 ya ce yana iya yin kokon kala-kala ya basu launi da dandano daban-daban

- A cewar dalibin dake karatu a jami'ar NOUN, yace yana kokari wajen ganin ya fadada kasuwancinsa sannan kuma ya kara tsaftace wajen sana'arsa idan ya samu kudi

Akwai alfahari akan kowacce sana'a mutum yake yi a rayuwa idan har kuwa ba ta haramun bace. Kada wanda yaji kunyar abinda yake yi yana samun na kashewa.

Wani dalibin aji daya a jami'a mai suna Jimoh John Yakubu, ya dauki sana'arshi da matukar muhimmanci, inda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar 9 ga watan Agusta.

Dalibin Najeriya da yake amfani da sana'ar siyar da Koko yake biya kanshi kudin karatu a jami'a
Dalibin Najeriya da yake amfani da sana'ar siyar da Koko yake biya kanshi kudin karatu a jami'a
Asali: Twitter

Yakubu ya ce sana'ar koko ita ce hanyar samun abincin shi, kuma da ita yake amfani wajen biyan bukatunshi da kuma biyawa kanshi kudin makaranta.

Dan kasuwar mai shekaru 21 dan asalin jihar Ado Ekiti ya kara da cewa yana yin kokon launi daban-daban, sannan ya bashi dandano daban-daban.

KU KARANTA: Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa

A hoton da ya wallafa a shafinsa na Twitter, an gano manyan baho da aka cika da kokon, sannan a can gefe kuma ga injin da yake malkada abinda yake kokon da shi.

Wannan abu da ya wallafa ya sanya mutane suka yi ta yaba masa, inda har wani ya bukaci su zama abokai su cigaba da sana'ar tare.

A karshe ya yiwa duka mutanen da suka yi masa fatan alkhairi, sannan kuma ya kuma mayarwa mutanen da suka ce wurin da yake aikin babu tsafta.

Ya ce: "Nagode kwarai da gaske da shawarwarin ku. Amma haka koko yake yana kama jikin abu idan ya zuba. Zanyi kokari nan gaba naga na gyara wajen yayi tsafta sosai idan na samu kudi. Nagode."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel