Facebook zai rabawa kananan 'yan kasuwa a Najeriya tallafin N500m

Facebook zai rabawa kananan 'yan kasuwa a Najeriya tallafin N500m

- Kamfanin manhajar dandalin sada zumunta na 'Facebook' zai rabawa kananan 'yan kasuwa 781 a Najeriya tallafin miliyan N500

- Facebook ya ce zai bayar da tallafin kudin ne domin bawa kananan 'yan kasuwa samun damar warwarewa daga matsin tattalin arziki da annobar korona ta haifar

- Kamfanin Deloitte tare da hadin gwuiwar FATE Foundation da Afrigant ne zasu kula tare da raba tallafin ga kananan 'yan kasuwar da suka cancanta

A ranar Litinin ne kamfanin manhajar dandalin sada zumunta na 'Facebook' ya sanar da shirin fara rabawa kananan 'yan kasuwa 781 a Najeriya tallafin miliyan N500.

Shirin bayar da tallafin na daga cikin tsarin kamfanin 'Facebook' na rabawa kananan 'yan kasuwa 30,000 a kasashen duniya fiye da 30 tallafin dalar Amurka $100m, kamar yadda ya sanar a farkon shekarar 2020.

Har yanzu manhajar 'Facebook' ce a gaba idan ana maganar kamfanonin da suka mallaki manhajojin da ake yi wa 'kudin goro' ta hanyar kiransu da sunan dandalin sada zumunta.

Kamfanin 'Facebook' ya sanar da cewa zai bayar da tallafin ne domin taimakawa jama'a wajen farfadowa daga kangin matsin tattalin arziki da aka shiga sakamakon bullar annobar korona.

Facebook zai rabawa kananan 'yan kasuwa a Najeriya tallafin N500m
Mark Zuckerberg; shugaban kamfanin manhajar Facebook
Asali: UGC

A cewar kamfanin, an zabi bayar da tallafin ga kananan 'yan kasuwa ne saboda sun fi jin jiki sakamakon tasirin annobar korona.

DUBA WANNAN: Ba kanta: Tattalin arzikin Nigeria ya karye

Kamfanin Deloitte tare da hadin gwuiwar FATE Foundation da Afrigant ne zasu kula tare da raba tallafin, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

"Za a bayar da tallafin kudi da damar tallata hajar 'yan kasuwa kyauta domin taimakawa kananan 'yan kasuwa a yayin da suke shirin farfadowa bayan kalubalen da wannan shekarar ta zo da shi," a cewar sanarwar.

Ma su son neman tallafin zasu iya ziyartar shafin www.facebook.com/grantsforbusiness daga ranar 24 ga watan Agusta domin samun karin bayani da kuma sanin sauran ka'idoji da sharuda.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel