Ba a rasa na Allah: Matar aure ta mayar da naira miliyan 14 da aka yi kuskuren tura mata ta banki

Ba a rasa na Allah: Matar aure ta mayar da naira miliyan 14 da aka yi kuskuren tura mata ta banki

- Wata matar aure a jihar Enugu mai suna Josephine Nchetaka Chukujama Eze, ta mayar da N13,946,400 da aka yi kuskuren tura asusunta na banki daga wani kamfani a jihar Legas

- Bayan Josephine ta karbi wannan kudi a ranar Litinin 3 ga watan Agusta, ta je ta sanar da mijinta halin da ake ciki

- Duk da dai wasu mutanen sun nuna rashin jin dadinsu akan mayar da kudin, mijinta Eze, yayi ta yaba mata

Wata mata daga jihar Enugu mai suna Josephine Nchetaka Chukujama Eze, ta nuna ainahin adalci bayan ta mayar da kimanin naira miliyan goma sha hudu da aka yi kuskuren aikawa zuwa asusunta na banki.

Mijinta wanda yake dan jarida ne kuma lauya, Chukujama Eze, ya bayyana haka ga News Express yayin da yake yabon matarshin akan abin kirkin da tayi.

Ba a rasa na Allah: Matar aure ta mayar da naira miliyan 14 da aka yi kuskuren tura mata ta banki
Ba a rasa na Allah: Matar aure ta mayar da naira miliyan 14 da aka yi kuskuren tura mata ta banki
Asali: Facebook

A wata takarda da ya aikawa jaridar, ya ce zai taya ta farin ciki ba wai saboda ranar ita ce ranar haihuwarta ba, sai dan kawai tayi abin da yake alfahari da ita.

Mijin yace lamarin ya faru a ranar Litinin ne uku ga watan Agusta, a lokacin da Josephine take shagon gyaran gashi, sai taji wayarta tayi kara.

KU KARANTA: Mace mai kamar maza: Ta yi watsi da daukar 'yan aiki ta zage dantse tana gina gidanta da kanta

A lokacin matar mai yara uku bata duba wayarta ba, sai daga baya, bayan ganin wannan makudan kudade ya sanya ta kira mijinta ta sanar da shi.

Bayan bincike an gano cewa wannan kudi na wani kamfani ne a jihar Legas mai suna Sankiya Global Investment, inda suka bukaci bankin Josephine da su mayar da kudin.

Eze ya ce bayan wasu mutane sunji wannan magana sun nuna rashin jin dadinsu kan mayar da kudin da matar tayi. Yace ma'aikatan bankin sunyi farin ciki sosai da wannan abin kirki da matarshi tayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel