An yabawa wani saurayi da ya ciyar da kauye guda dake dauke da yara kanana 120

An yabawa wani saurayi da ya ciyar da kauye guda dake dauke da yara kanana 120

- Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Bi Phakatsi ya ciyar da wani kauye da yake dauke da yara 120

- Wannan abin kirki da yayi ya fito fili ne bayan wallafa wani bidiyo da yayi a shafinsa na Facebook din, inda ya samu mutane masu dumbin yawa suka kalla

- Haka kuma saurayin yayi alkawarin aikawa da matar da ta taimaka ta dafa abincin da kudi sama da naira dubu dari

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Bi Phakathi ya sanya farin ciki a zuciyar al'umma. A wannan karon ya ciyar da wani karamin kauye ne da yake dauke da yara 120 sannan kuma ya bayar da tsabar kudi har N111,578. Bi Phakathi yayi suna matuka akan abubuwa na alkhairi da yake yi, yayin da shafinsa na Facebook yake cike da bidiyon shi na abin alkhairi da yake yiwa al'umma.

An yabawa wani saurayi da ya ciyar da kauye guda dake dauke da yara kanana 120
An yabawa wani saurayi da ya ciyar da kauye guda dake dauke da yara kanana 120
Asali: Facebook

A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa a wannan makon, Bi Phakathi an gano shi yana magana da wata mata wacce ta dafa wannan abinci ga wadannan bayin Allah, kafin daga baya ya bayyanawa yaran kanshi.

Yaran sun taru a wani wuri, inda aka bukaci su tsaya nesa da juna kowanne da takunkumi a fuskarshi.

KU KARANTA: Yadda na bar kiwon shanu na zama babban dan jarida - Umaru Sanda ya wallafa labarin shi mai ban sha'awa

Matar da ta dafawa yaran Abinci ta kidime a lokacin da Bi Phakathi ya bayyana mata cewa zai tura mata kudi sama da naira dubu dari ta banki. Da farko ya fara rabawa yaran alawa ne kafin daga baya ya bude motarshi ya fito da shinkafa da mai ya dinga raba musu.

An yabawa wani saurayi da ya ciyar da kauye guda dake dauke da yara kanana 120
An yabawa wani saurayi da ya ciyar da kauye guda dake dauke da yara kanana 120
Asali: Facebook

Mutane da dama sun ji dadin wannan abin alkhairi da bawan Allah din yayi, inda suka dinga yaba masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel