Daga yanzu haramun ne amfani da wayar salula a gidajen mai - Hukumar DPR

Daga yanzu haramun ne amfani da wayar salula a gidajen mai - Hukumar DPR

Hukumar arzikin man fetur DPR ta haramtawa masu mota amfani da wayoyin salula yayinda suka je sayan mai a gidajen sayar da mai domin kiyaye afkuwar gobara.

Jami'in gudanar da ayyukan hukumar na Osun, Olusegun Daboh, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai a Osogbo ranar Litinin cewa yin waya a gidan mai na da hadari saboda man fetur na iya kama wuta.

Mr Daboh ya yi kira da direbobi su tabbatar da cewa sun kashe motocinsu kafin su fara shan mai.

Ya gargadi yan kasuwan man fetur marasa lasisi, da masu ha'inci ta hanyar juya mitan injin sayar da mai cewa za'a ci su tara.

Ya yi kira ga mutane su shigar da karan gidajen mai masu ha'inci ofishin hukumar DPR.

Daboh ya kara da cewa jami'anta za su cigaba da sintiri gidajen mai domin tabbatar da cewa ana bi dukkan dokoki da ka'idojin da aka gindaya.

Ya shawarci al'umma su rika duba tukunyar iskar gas dinsu akai-akai domin yiwuwar yoyo saboda gudun mumunar gobara.

KU KARANTA: Kwana 4 bayan ziyarar SLS, Sarkin Musulmi ya kai El-Rufa'i ziyara

Daga yanzu haramun ne amfani da wayar salula a gidajen mai - Hukumar DPR
Daga yanzu haramun ne amfani da wayar salula a gidajen mai - Hukumar DPR
Asali: UGC

A ranar 7 ga Yuli, 2020, Ana tsaka da gudanar da aiki, kwatsam wuta ta kama a daya daga cikin cibiyoyin hako mai na kamfanin man fetur na kasa, NNPC, lamarin da ya janyo mutuwar ma'aikata bakwai nan take.

Kamfanin NNPC a ranar Laraba ya sanar da cewa, wata wuta da ta tashi a daya daga cibiyoyinta na hako man fetur da ke gabar Kogin Benin, ta yi sanadiyar salwantar rayukan ma'aikata bakwai.

Babban jami'in sadarwa da kula da sashen hulda da al'umma na kamfanin, Kenni Obateru, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Ya ce "wannan mummunan tsautsayi ya auku ne a ranar Talata yayin dasa wani tsani a gabar Kogin Benin wanda zai samar da wani dandamali a matsayin hanyar shige da fice yayin hako mai."

"Abin takaici ne mun yi asarar rayukan ma'aikata bakwai."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel