Yanzu-yanzu: Kwana 1 bayan ziyarar SLS, Sarkin Musulmi ya kaiwa El-Rufa'i ziyara

Yanzu-yanzu: Kwana 1 bayan ziyarar SLS, Sarkin Musulmi ya kaiwa El-Rufa'i ziyara

Kimanin sa'o'i 24 da ziyarar tsohon sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, zuwa wajen Gwamna Nasir El-Rufa'i, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III ya dira jihar Kaduna don kawo nasa ziyarar.

Mai alfarma sarkin Musulmi ya dira gidan gwamnatin Kaduna misalin karfe 12: 20 na rana a yau Litinin, 24 ga Agusta, 2020.

Ya samu tarba daga sakataren gwamnatin jihar, Balarabe Abbas; shugaban ma'aikatan El-Rufa'i, Muhammad Sani Dattijo; da kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan.

KARANTA WANNAN: Daga yanzu haramun ne amfani da wayar salula a gidajen mai - Hukumar DPR

Yanzu-yanzu: Kwana 4 bayan ziyarar SLS, Sarkin Musulmi ya kai El-Rufa'i ziyara
Yanzu-yanzu: Kwana 4 bayan ziyarar SLS, Sarkin Musulmi ya kai El-Rufa'i ziyara
Asali: Twitter

A jiya, Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya isa jihar Kaduna da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya a karon farko bayan tube masa rawani a watanni biyar da suka gabata.

Dubban masoya da masu fatan alheri ga tsohon sarkin Kanon sun fito da safiyar Lahadi inda suka yi cincirindo don masa barka da zuwa.

Karon karshe da Sanusi ya ziyarci jihar Kaduna shine lokacin bikin murnar cikar gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, shekaru 60 a duniya.

A lokacin da aka tube rawanin basaraken a ranar 9 ga watan Maris na 2020, El-Rufai ya nada Sanusi a matsayin shugaban jami'ar jihar Kaduna kuma mataimakin shugaban majalisar karfafa kasuwanci ta jihar.

Babban mataimaki na musamman ga basaraken, Dr Suleiman Shinkafi, ya ce tsohon sarkin zai kwashe mako daya a birnin Kaduna inda zai dinga karbar bakin da ke son ganinsa.

"Tun bayan tube masa rawani, jama'a da yawa sun nuna bukatar son kai masa ziyara a Legas. Amma basaraken ya yanke hukuncin saukake musu wahalar zuwa har jihar Legas ganinsa," ya jaddada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel